Daga Ibrahim Muhammad, Kano Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmad Tunubu akan yaɗa labarai, Malam Abdul'azeez Abdul...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmad Tunubu akan yaɗa labarai, Malam Abdul'azeez Abdul'azeez ya bayyana cewa tsohon tsarin da ake a kai na harajin sayayyar kayayyaki da ake kira "VAT Value added Tax," shi ne wanda ba ya taimakon jihohin Arewa yadda ya kamata, domin jihohin da suke da hedikwatar manyan kanfanoni ne suka fi amfanar kusan dukkanin kuɗi mafi tsoka na harajin.
Abdul'zeez ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da manema labarai a Kano, inda ya ce su kuma sauran jihohi, musamman waɗanda su ne ke da mafiya yawan al'umma, waɗanda a nan ne aka fi yin hada-hadar sayen kayayyakin, amma saboda ba a nan ne hedikwatar kamfanoni masu sarrafa kayan suke ba, sun zama tamkar ana barin su da ladan kuturun bawa ne kawai wajen amfanar harajin.
A nan ya kafa misali da cewa, jihar Kano abin da take karɓa bai taka kara ya karya ba daga tsarin harajin, duk da tana da ɗimbin mutane, amma jihohin Legas, Ribas, Oyo, Ogun inda a nan ne kamfanonin suke, sai ka ga su suke ɗaukar kaso mafi tsoka.
AbdulAzeez Abdulazeez ya ƙara da cewa, ko a watan 10 da ya gabata, jihohi huɗu kaɗai, wato Legas, Ribas da Oyo da babban Birnin tarayya su suka kwashe kaso 70 na kason harajin VAT da aka tara a watannin baya.
Ya ce don haka ita wannan doka da shugaban ƙasa ke so a gyara, yanzu da wasu mutane ba su fahimci amfanin ta ba, abin da ake so a yi shi ne, ya zama cewa ana duba biyan harajin "VAT" ta duba daga inda kuɗin ya fito, ba wai a ina ne hedikwatar kamfanin da suke zuwa su biya harajin ba.
Ya ce misali, a na iya samun wani kamfanin sadarwa na waya na da hedikwatarsa ke Legas, amma in aka duba nawa mutanen Kano suke kashewa wajen sayen kati ta yin waya da layin kamfanin, za a duba wannan yawan adadin ne, a biya masa haraji a ba jihar Kano kaso mafi tsoka a ciki, ba kamar yadda ake yi yanzu ba, saboda kawai hedikwatar kamfani na waje sai su sami kaso mafi tsoka.
Abdul'azez ya ce wannan shi ne sabon tsarin da za a zo da shi wanda kuma ta yin haka ɗin, za a sami sauƙi matuƙa da gaske.
Malam Abdul'azeez Abdula'azez ya ce, Tsarin zai amfane mu a Arewa, wanda mu ne ke da mafi yawan al'umma, Ya kamata ma mu fi kowa jin daɗin wannan tsarin da zai canza ya dawo da kuɗaɗe ga jihohi da ake sayen kayan, ba wai ga jihohi da su ne hedikwata na kamfanoni da ke samar da kayayyaki ba."

No comments