Daga Ibrahim Muhammad, Kano Alhaji Sani Baba, shugaban ne masu sayar da taki da sauran kayan amfanin gona na gidan Aminu Ɗantatta a kasuwar ...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Alhaji Sani Baba, shugaban ne masu sayar da taki da sauran kayan amfanin gona na gidan Aminu Ɗantatta a kasuwar Galadima, sannan kuma shugaban jam'iyyar NNPP na mazaɓar Dala, ya bayyana cewa babu wani abu da zai iya girgiza tafiyar Kwankwasiyya yankin Ƙaramar Hukumar Dala ta jihar Kano.
Haka kuma Alhaji Sani Baba ya bayyana Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Dala Hon. Suraj Imam da cewa mutum ne mai ƙokari, wanda kowa ya sanshi a haka, don haka zai kawo gagarumar ci gaba a yankin.
Alhaji Sani Baba ya bayyana hakan ne a zantawar sa da 'yan jarida a taron rantsar da Ƙansiloli da aka yi a sakatariyar Ƙaramar Hukumar ta Dala, inda ya yi addu'ar Allah ya taimaka ya kawo waɗanda za su yi aiki da shi jajirtattu matasa da aka ɗora ƙwarya a gurbin ta.
Shugaban jam'iyyar NNPP na mazaɓar Dala ya yi fatan yadda aka zaɓo Ƙansilolin da masu bai wa shugaban Ƙaramar Hukumar Dala shawara da sauran ma'aikat, Allah ya sa su riƙe amana, su kuma samu shawara tagari daga jana'a.
A ƙarshe Alhaji Sani Baba ya ce a tsarin Kwankwasiyya dama sun saba ganin rikice-rikice da ake ƙullowa, kuma wannan ma ƙarami ne a ciki, kuma ba zai taɓa musu tasirin siyasar Kwankwaso a Dala ba ko ya kawo musu nakasu ba.

No comments