Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana fitaccen ɗan kasuwar nan na qasar nan ɗan asalin jihar Katsina, Alhaji Barau Dahiru Mangal da cewa U...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana fitaccen ɗan kasuwar nan na qasar nan ɗan asalin jihar Katsina, Alhaji Barau Dahiru Mangal da cewa Uba ne ta fannonin Kasuwanci da siyasa, kuma babban jagora ne a harkar kasuwanci da yake bada gudunmuwa ga ci gaban al'umma, wannan abin a yaba ne.
Alhaji Sarki Usman Dahiru, Shugaban Kamfanin DANMARNA Petroleum ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a fadar Sarkin Kano a lokacin da ya halarci bikin ɗaurin auren ɗan Alhjaji Ɗahiru Mangal da 'yar tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso.
Ya yi nuni da cewa ɗaurin auren wata rana ce ta musamman mai cike da tarihi ga al'ummar Kano, inda aka tara ɗimbin jama'a suka shaidi auren tsakanin Iyalan na Kwankwaso da na Alhaji Ɗahiru Mangal da aka zo daga sassa daban-daban na ciki da wajen ƙasar nan.
Shugaban Kamfanin man fetur na DANMARNA ya ce Kano babbar uwa ce a ƙasar Hausa, don haka wannnan taro na ɗaurin aure ya ƙara fito da martabar ta da karamcin Kanawa wajen karɓar baƙi.
Alhaji Sarki Usman Dahiru ya yaba wa Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa irin ayyuka da ya gani ana aiwatarwa na ci gaban jihar Kano a fannoni da dama.
Alhaji Ɗahiru ya Jaddada cewa wannan aure da ya haɗa iyalan ɗan siyasa da na ɗan kasuwa, da ma tskaninsu tafiya ce da suke yi ta Ɗanjuma da Ɗanjumai, domin kasuwanci na tafiya da siyasa.
Ya ce, yanzu tafiya ce ta cuɗar juna, don haka wannan abin alfahari ne da farin ciki bisa gagarumin wannnan haɗi da aka yi, komai ya yi daidai. Muna yi musu fatan alkahiri da fatan samun zaman lafiya da zuriya tagari.

No comments