Daga Hussaini Yero, Gusau Uwargidan Gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta yi kira ga sabbin shugabannin Ƙananan Hukumomi d...
Daga Hussaini Yero, Gusau
Uwargidan Gwamnan jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal ta yi kira ga sabbin shugabannin Ƙananan Hukumomi da su bai wa zaɓaɓɓun Mata Kansiloli dama yadda ya kamata don ci gaban al'umma a mazaɓunsu.
Hajiya Huriyya Dauda ta bayyana haka ne jim kaɗan bayan rantsar da Shugabanin Ƙananan Hukumomi da Kansiloli da ya gudana a Jihar ta Zamfara.
Huriyya Dauda ta kuma yi ƙarin haske akan samun zaɓaɓɓun Kansiloli Mata a kowace Ƙaramar Hukumar, ta ce abin a yaba wa Jami'yya PDP ne da al'ummar Jihar Zamfara, wanda a cewar ta wannan shi ne karon farko a tarihin Zamfara da aka zaɓi Mata su zamo cikin Majalisar zartartarwa a cikin Ƙananan Hukumomi ta Zamfara.
"Kuma babu shakka zaɓar Mata a matsayin Kansiloli gwaji ne gare mu kuma da yardar Allah za su yi abun da ya kamata dan ansan Mata da tausai da rikon amana, kuma In sha Allah wannan ne zaiba Mata damar yin Shugabancin Karamar Hukumar da yardar Allah a nan gaba," inji Huriyya Dauda.
Akan haka ne ta yi kira da babbar murya ga su Shugabanin Kananan Hukumomi da su yi adalci wajen tafiya da su kafaɗa da kafaɗa domin samun nasara da ci gaban Jihar Zamfara.
Ta ce, "Su kuma zaɓaɓɓun Kansiloli Mata su zamo kallabi tsanin rawuna wajen samar da ci gaban mazaɓun su ta kowane sashe, al'umma su gano cewa, Mata ma ashe ba a bar su a baya ba wajen iya wakilcin al'umma a Majalisar Kananan Hukumomi.

No comments