Daga Ibrahim Muhammad, Kano Shugaban Ƙaramar Hukumar Dala ta jihar Kano, Hon. Suraj Ibrahim Imam ya jagoranci rantsar da Kansuloli masu gaf...
Shugaban Ƙaramar Hukumar Dala ta jihar Kano, Hon. Suraj Ibrahim Imam ya jagoranci rantsar da Kansuloli masu gafaka da masu ba shi shawara na Ƙaramar Hukumar a ranar Litinin da ta gabata.
Taron rantsuwa, wanda ya gudana a harabar sakatariyar, ya sami halartar jagororin siyasar yankin, ƙarƙashin shugaban jam''iyyar NNPP na Dala, wanda shi ne jagoran Kwankwasiyya na yankin, Alhaji Ɗayyabu Ahmad Maiturare da Kwamishinan bibiyar ayyuka na jihar Kano, Hon. Ibrahim Ali Namadi Dala da sauran masu ruwa da tsaki.
Da yake jawabin bayan rantsar da Kansilolin masu gafaka da masu ba shi shawara, shugaban karamar hukumar ta Dala ya ja hankalin waɗanda aka rantsar su yi aiki da gaskiya da amana wajen sauke wannan nauyi da aka ɗora musu.
Ya bayyana cewa su a matsayinsu na 'yan Kwankwasiyya tamkar iyali ɗaya suke, sannan koda wani ya yi kuskure ya bar cikin gida ya kuma gane kuskure ya dawo, suna son kayansu, za su ci gaba da tafiya tare da shi domin bunƙasa ci gaban Dala da jihar Kano baki ɗaya.
Kansiloli masu gafaka guda Bakwai da shugaban na Dala Suraj Imam ya rantsar, akwai tsohon Kantoman riƙo na Dala, Hon. Auwalu Abdulƙadir hasken Dala a matsayin Kansilan mai gafaka na Ilimi, da Aminu Mamman Yaro Kansilan lafiy, da Nura Ibrahim PRS, da Binta Halliru Musa Wash and Water da Bello Abdulkadir na community.
Haka kuma cikin mutum 10 da shugaban ya rantsar a matsayin masu ba shi shawara, akwai Hon. Kabiru Kaigama mai ba shi shawara akan siyasa, da Malam Inyas mai ba shi shawara kan addini, da Hajiya Ummu Alasan Kofar Ruwa mai bada shawara kan muhalli.
Taron dai ya sami halartar ma'aikatan Ƙaramar Hukumar da suka haɗa da Daraktar Mulki, Hajiya Binta Abdullahi.

No comments