Daga Ibrahim Muhammad, Kano Sa'in Kano Arc. Ali Mukhtar Adnan ya gode wa Sarkin Kano Khalipha Muhammadu Sanusi bisa tabbatar masa da sar...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Sa'in Kano Arc. Ali Mukhtar Adnan ya gode wa Sarkin Kano Khalipha Muhammadu Sanusi bisa tabbatar masa da sarautar Hakimin Makoɗa, inda ya yi alƙawarin bai wa kowa haƙƙinsa, tare da bunƙasa zaman lafiya tsakanin al'ummar Makoɗa.
Don haka sai Sa'in ya nemi al'umma su taimaka da yi masa addu'a domin sauke nauyin da aka ɗora masa na gudanar da abin da ya kamata cikin adalci.
Arc.Ali Muktar Adnan ya yi nuni da cewa shi al'amari na naxin sarauta kowa mai martaba ya naɗa a wani matsayi sai an binciki halinsa kafin a yi masa, kuma daga shaida da Sarkin Kano Muhammad Sanusi ya bayar a kansa, da alama akwai abubuwa da aka yi nazari aka ga zai iya ɗaukar wannan nauyi, domin an sha ɗaukar nauye-nauyen nan ta fuskoki da dama, kuma an sami nasara, wannan ma suna da yaƙinin samun nasara da yardar Allah.
A ƙarshe Sa'in na kan, Hakimin na Makoɗa Arc. Ali Muktar Adnan ya yi kira ga al'ummar Makoɗa akan su zauna lafiya, kuma duk abin da za a yi shi bisa adalc, shi ne ginshiƙin zaman lafiya saboda haka a shirye yake, ya bi umurnin Sarki na cewa a zauna a yi adalci, kuma a tabbatar an bai wa kowa haƙƙinsa.
No comments