Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Naɗa Sarkin Yamma Na Farko A Masarautar Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Sabon Sarkin Yamman Kano Alhaji Abdullahi Sarki Muhammad ya bayyana godiyarsa bisa  damar da Allah ya ba shi na ...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Sabon Sarkin Yamman Kano Alhaji Abdullahi Sarki Muhammad ya bayyana godiyarsa bisa  damar da Allah ya ba shi na zaɓensa a cikin mutane da yawa, ba domin ya fi wani ba, amma Sarkin Kano Malam Muhammad  Sanusi ya ga ya cancanta ya naɗa shi a sarautar Sarkin Yamman, wanda shi ne na farko a masarautar.

Ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidansa jim kaɗan bayan naɗin da aka yi masa.

Alhaji Abdullahi Sarki Muhammad ya ƙara da godiya ga Allah bisa wannan sabuwar sarauta da aka ba shi wacce ba a taɓa yinta a Kano ba, ita ce    ta farko da Allah ya nufa shi aka soma yi wa a wannan lokaci.

Sabon Sarkin Yamman na masarautar Kano Alhaji Abdullahi Sarki Muhammad ya ce kasancewar  sarautar baƙuwa ce a Kano, suna shirye da yin biyayya da yin ayyukan da mai martaba Sarki Malam Muhammad Sanusi zai ɗora musu nauyin gudanarwa.

Ya ce muhimmin abin da za su yi shi ne su taimaka wajen bayar da shawara wajen yadda za a tafi da mulki a ƙasar Kano, yanzu abin da za su yi ke nan, kuma yana matuƙar farin ciki da shi ne  ya soma rabauta da sarautar. 

A ƙarshe Alhaji Abdullahi Sarki Muhammad ya  gode wa dukkan al'umma na gida da na waje waɗanda suka zo da wanda suka aiko da saƙon fatan alkhairi. 

 

No comments