Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ƙungiyar 'yan jarida ta ƙasa, sashen wakilan kafafen yaɗa (Correspondent Chapel) na Jihar Kano ta bayar da...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Ƙungiyar 'yan jarida ta ƙasa, sashen wakilan kafafen yaɗa (Correspondent Chapel) na Jihar Kano ta bayar da sanarwar ƙaurace wa yaɗa labaran ayyukan gwamnatin jihar har sai abin da hali ya yi.
A wata sanarwa da ya fitar, shugaban ƙungiyar, Aminu Ahmad Garko ya ce bayyana cewa sun yanke shawarar ƙaurace wa duk wasu harkokin da suka shafi Gwamnatin Jihar Kano nan take.
Ya ce, an ɗauki wannan matakin ne saboda irin cin zarafin da gwamnatin Kano da jami’anta suke yi wa mambobin ƙungiyar a jihar, musamman a yayin gudanar da ayyukansu .
Ya ce, "Duk da ƙokarin da muka yi na tattaunawa da gwamnati da jami'anta don magance waɗannan matsalolin, amma ba mu ga wani ci gaba ba.
Mambobin ƙungiyar sun ci gaba da fuskantar tsangwama, tsoratarwa har ma da cin zarafi a yayin gudanar da ayyukansu.
"Musamman abin ya shafi yadda gwamnati ta fifita wadanda ba kwararru ba akan ‘yan jarida da suke da kwarewa da su, inda hakan ya sanya ya zama wata manufa ta jiha ta ware wadanda suka fi dacewa da aikin.
"Sakamakon haka, muna sanar sa cewa ba za mu sake shiga taron manema labarai ba, ba za mu ba da labari ba, ko kuma yin hira da jami’an jihar har sai mun ga tabbatar da ‘yancin ‘yan jarida da kare lafiyar su.
Takardar kuma ta umurcri ɗaukacin mambobin ta su bi wannan umurrn, su kasance tare da mu a wannan nuna rashin amincewa da yadda ake yi wa membobin su a jihar Kano.
A ƙarshe ya ce, "Mun yi imanin cewa 'yan jarida suna da mahimmanci ga Dimokraɗiyy, kuma ba za su yi ƙasa a gwiwa ba yayin da ake cin zarafi da kuma tsoratar da mambobin mu."
No comments