Hukumar da ke Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa, EFCC, ta tattaro wasu gungun masu bincike domin binciken zargin karkatar ...
Hukumar da ke Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Zagon Ƙasa, EFCC, ta tattaro wasu gungun masu bincike domin binciken zargin karkatar da Naira Biliyan 423 da Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai da wasu fitattun mutane a gwamnatin sa suka yi.
Masu binciken dai za su gayyaci Tsohon Gwamnan domin yi masa wasu zafafan tambayoyi.
Sauran waɗanda za a yi wa tambayoyi sun haɗa da mutanen da suka riƙe muƙamin Kwamishinonin kuɗi tsakanin 29 ga Mayu, 2015, da 29 ga Mayu, 2023; dukkan manyan Akantoci Janar na tsawon shekaru takwas da ya yi yana mulki, da kuma shugabannin Hukumar Tara Haraji ta Jihar Kaduna (KADIRS) daga 2018 zuwa 2023.
Sauran sun haɗa da; dukkanin tsoffin manajojin gudanarwa na Kamfanin Raya Kasuwar Kaduna a tsakanin 29 ga Mayu, 2015, zuwa 29 ga Mayu, 2023, da tsoffin manajojin hukumar kula da hanyoyin Kaduna (KADRA) daga ranar 11 ga Oktoba, 2017, zuwa Nuwamba 2021, amma banda Amina Ja'afar Ladan, wacce ta riƙe muƙamin wata guda a taƙaice.
“Mun samu takardar koke daga wata ƙungiya mai zaman kanta. Don haka, mun fara bincike a kan batutuwan da aka gabatar a cikin takardar koken.
“Rahoton kwamitin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna shi ma yana da amfani. Nan ba da jimawa ba za mu gayyaci El-Rufai da wasu ’yan tawagarsa domin yi musu tambayoyi.
"Rahoton Majalisar ya kafa tushe mai ƙarfi ga binciken da tawagarmu za ta gudanar" in ji wata majiya.
No comments