Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Yi Babban Rashi

Hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta jihar Kaduna ta bayyana rasuwar Darakta mai kula da sashen harkokin kuɗi da mulki, Hajiya Hannatu Zaila...

Hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta jihar Kaduna ta bayyana rasuwar Darakta mai kula da sashen harkokin kuɗi da mulki, Hajiya Hannatu Zailani.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi ya fitar, ta bayyana cewa Hajiya Hannatu ta rasu ne jiya Asabar a wani asibiti da ke Kaduna bayan wata gajeruwar rashin lafiya.

Sanarawar ta ci gaba da bayyana cewa "Hajiya Hannatu ta kasance jajiratacciyar ma'aikaciyar gwamnati ce da ta jima tana aiki da wannan Hukumar. Ta fara aikin ta ne tun a cikin shekarar 1990, inda tafiya ta yi tafiya har ta kai matsayin Darakta mai kula da sashen harkokin kuɗi da mulki. Ta ma taɓa riƙe shugabancin Hukumar a tsakanin shekarun 2019 zuwa 2022.

"Ba za mu taɓa mantawa da kyakkywan shugabanci da jajirjicewa a aiki irin na Hajiya Hannatu ba. Muna miƙa matuƙar ta'aziyyar mu ga iyalai, 'yan uwa, abokan arziki da abokan aiki. 

"Hajiya Hannatu ta rasu ta bar mijinta da 'ya'ya. Tuni aka yi mata jana'iyaza a maƙabartar Unguwar Sarki, Kaduna," in ji sanarwar. 

 

No comments