Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana cewa al'ummar Ƙaramar Hukumar Dala ta jihar Kano sunyi matukar sa'ar samun matashi mai kiahi...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana cewa al'ummar Ƙaramar Hukumar Dala ta jihar Kano sunyi matukar sa'ar samun matashi mai kiahin jama'ar sa, bisa samun Aminu Mamman Yaro, wanda kullum tunaninsa ya ta'allaƙa ne ga son ci gaban matasa da Mata, musamman masu ƙaramin ƙarfi.
Ɗaya daga cikin manyan mantan da ke wannan yanki, Hajiya Hadiza Balaraba Mammam Yaro ce ta bayyana haka lokacin da ta ke zantawa da 'yan jarida a yayin taron tallafa wa waɗanda ta jagoranta aka koya musu sana'oi a mumbayta.
Ta ce, Aminu Mamman matashi ne mai manufofi da dama na koya wa matas a sana'oi da ba su tallafi na dogaro da kai da ƙirƙirar wani ofishi da zai riƙa sasanta rikicin aure, duba da yawan mutuwar aure da ake samu saboda yana jin zafin rabuwar aure da ke jawo naƙasu a tarbiyya da ilimin yara.
Ta ce, ya zo da manufa ta mayar da Dala sabuwa da za ta zama abin koyi ga Ƙananan Hukumomin da suke Kano, ta irin abubuwa da yake yi, domin shi Mutum ne mai kishin Dala.
Ta ƙara da cewa, yanzu ma al'ummar Dala ne suke ta neman ya fito ya nemi takarar Ƙaramar Hukumar Dala, domin sun ga ko da ba shi da muƙami, kullum taimako yake yi, kullun yana da kyakkyawar mu'amala da mutane.
Hajiya Hadiza Balaraba Mamman Yaro ta ce, su al'ummar Dala a shirye su ke su ba shi goyon bayan da yakamata domin a ciyar da Ƙaramar Hukumar Dala gaba, ya cimma manufar sa ta zama sabuwa da za ta zama abin koyi wajen ci gaban al'umma da matasa.
No comments