Daga Ibrahim Muhammad. Kwamishina a Hukumar Fansho ta jihar Kano, Alhaji Hasan Muhammad Aminu ya ce, duba da halin da ake a ciki bai kamata ...
Daga Ibrahim Muhammad.
Kwamishina a Hukumar Fansho ta jihar Kano, Alhaji Hasan Muhammad Aminu ya ce, duba da halin da ake a ciki bai kamata a ce mutum ya ci ya sha ba, amma ɗan'uwansa ko maƙwabcin sa, balle maraya da yake unguwar su a ce bai samu ya ci ba.
Alhaji Hassan Muhmmad Aminu bayyana haka ne a wajen taron ƙungiyar tallafa wa gajiyayyu da marayu ta Gandun Albasa da ke Kano, inda ya yi nuni da cewa idan matsala ta tashi, ba wai wannan ne shi kaɗai ke da matsalar ba.
Ya ce, "sai ka dubi kanka idan kai ne a wannan yanayin ya zaka sami kan ka a ciki. Saboda haka muhimmin abu ne taimaka wa juna."
Kwamishinan ya ce saboda irin kyakkyawan hali na Gwamnan Jihar Kano da tausayawa Marayu, ana dafa wa a baiwa marayu da suke zuwa tantance takardun Fansho na magabatansu da suka rasu abinci don rage musu raɗaɗin rayuwa.
No comments