Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Jami'an NAF Suka Cafke Ƙasurgumin Ɗan Ta'adda, Isah Abdul A Kano

Daga Musa Muhammad  Jami'an rundunar sojojin saman ƙasar nan ta NAF da aka tura yankin Durbunde ta Ƙaramar Hukumar Takai da ke jihar Kan...

Daga Musa Muhammad 

Jami'an rundunar sojojin saman ƙasar nan ta NAF da aka tura yankin Durbunde ta Ƙaramar Hukumar Takai da ke jihar Kano sun samu nasarar damƙe wani ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, ɗan kimanin shekara 35 mai suna Isah Abdul.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ta ƙasa, Edward Gabkwet ya saya wa hannu, ya bayyana cewa an samu wannan nasara ce a ranar 19 ga Faburairun nan na 2024 da misalin ƙarfe 6.30 na yamma a wani tsararren samame da suka kai wa maɓoyar Isah da jama'ar sa a yankin da garkuwa da mutane ya yi ƙamari, sakamakon wani bayanin sirri da suka samu. 

Sanarwar ta Edward Gabkwet ta bayyana cewa ya zuwa yanzu binciken su ya gano cewa Isah Abdul da tawagar sa ne ke da alhalin yin garkuwa da wani Yakubu Ibrahim Tagaho, wanda ake yi wa laƙabi da "Sarkin Noman Gaya," a ranar 6 ga watan Afrilun 2023 a gidan sa da ke garin Tagaho a Ƙaramar Hukumar Takai. Amma daga bisani bayan wata ɗaya a hannun su, Sarkin Noman ya samu kan sa sakamakon biyan kuɗin fansa na Naira Miliyan 30.

Haka kuma a cikin watan Disambar 2023, su dai waɗannan 'yan ta'adda sun kama wasu 'yan mata 2 'yan uwan juna, tare da wasu mutum 3 a wannan gari na Tagaho, inda daga bisani suka sake su bayan sun karɓi maƙudan kuɗaɗe. 

Rundunar sojin saman ta ci gaba da bayyana cewa Isah ne ke da alhakin yawancin kame-kamen mutane da ake yi a yankin, domin yana da dangantaka mai ƙarfi tsakanin sa da wasu sansanonin masu garkuwa da mutanen, irin dabar su  Danbul Fulaku, waɗanda su ma suka addabi Ƙaramar Hukumar ta Takai.

Rundunar ta ce yanzu haka Isah Abdul yana tsare a hannun ta ana gudanar da bincike, wanda da zarar ta kammala binciken ta, za ta miƙa shi ga Hukuma ta gaba don ci gaba faɗaɗa bincike.

 

No comments