Daga Ibrahim Muhammad, Kano Sarkin Kkano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira Hukumar hana fasa ƙwauri ta ƙasa akan su bar 'yan kasuwa ba ...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Sarkin Kkano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi kira Hukumar hana fasa ƙwauri ta ƙasa akan su bar 'yan kasuwa ba tare da tangwama ba, su gudanar da kasuwancin su, muddin ba su saɓa doka ba.
Sarkin ya yi kiran ne lokacin da mataimakiyar Kwanturola janar ta Hukuma, Sarauniya Ogbudu ta kawo masa ziyara a fadar sa da me Kano cikin makon nan.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma koka Mata da cewa jami'an na su na shiga kasuwa su karɓe kayan 'yan kasuwa ba bisa ƙa'ida ba. Ya Kuma nemi jami'an su riƙa zama da 'yan kasuwar domin wayar musu da kai akan irin kayan da doka ta amince a shigo da su da waɗanda ba a amince ba.
A jawabin ta, mataimakiyar Babbar Kwanturola Janar na ɗin, mai kula da shiyyar Kano, Kaduna, Jigawa da Katsina, Sarauniya Ogbudu ta ce ta zo Kano ne domin sanar da Sarkin cewa shugaban ƙasa ya bada umarni da su fitar da kayan abinci domin raba wa al’ummar ƙasa sakamakon matsin da ake fama da shi.
No comments