Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Zamba A ATM: Kotu Ta Ci Tarar Wani Matashi N30,000 A Bauchi

-Ina Tara Kuɗin Aure Ne -Mai laifin  Wata babbar kotu a garin Bauchi, ƙarƙashin Mai Shari'a M.A Shambu, a cikin watan Disambar da ya gab...


-Ina Tara Kuɗin Aure Ne -Mai laifin 

Wata babbar kotu a garin Bauchi, ƙarƙashin Mai Shari'a M.A Shambu, a cikin watan Disambar da ya gabata ta yanke hukuncin ɗaurin shekara ɗaya a gidan Yari ga wani matashi mai suna Ibrahim Abdullahi, ko kuma tarar Naira Dubu Talatin (N30,000) sakamakon kama shi da laifin canja wa wata mata katin ta na ATM a wurin cire kuɗi.

Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arzikin ƙasar nan zagon ƙasa da sauran zambar kuɗaɗe ta EFCC ta jihar Gombe ce ta gurfarnar da Abdullahi a gaban kotun bisa laifin sata da zamba. 

A yayin Shari'ar, Alƙalin ya karanta cewa, “kai Ibrahim Abdullahi, wani lokaci a cikin watan Satumbar 2023 a garin Bauchi ta jihar Bauchi, wanda kuma yana cikin hurumin wannan kotu, ka aikata satar kuɗi Naira Dubu Talatin (30,000), ta hanyar ɗauke katin ATM na wata mata mai suna Zainab Usman, ka yi amfani da bankin ta na UBA, wanda hakan ya saɓa ma sashe na 287 na dokar  Penal Code.”

Da ya ke yanke hukuncin, Mai Shari'a Shambu ya ɗaure Abdullahi ɗaurin shekara ɗaya a gidan kaso, ko kuma ya biya yarar Naira Dubu Ashirin, sannan ya biya wacce ya cuta kuɗin ta, Naira N30,000.

Wanda ake tuhumar ya amsa laifin sa, wanda hakan ta sa Lauyan Hukumar EFCC, A.B. Kware ya roƙi kotun da ta ɗaure wanda ake zargin. Sannan shi kuma Lauyan sa, Jamilu Salihu ya roƙi kotun da ta yi wa wanda ake zargin sassauci, musmman ganin cewa wannan ne karo na farko da ya aikata irin wannan laifi.

Abdullahi dai ya faɗa wannan matsala ne sakamakon koken da mai ƙara ta kai, ta na mai cewa a ranar 22 ga watan Nuwambar 2023 ta ga saƙo an  cire mata N30,000 daga asusun ta na UBA, alhali a akwai lokacin da ta je cire kuɗi a wani wurin cire kuɗi na ATM, inda ta tarar da Abdullahi, kuma har ya nemi ya taimake ta cirewa. 

Ta ce, lokacin da Abdullahi ya saka katin ta a na'urar cire kuɗin, sai ya ciro, ya ce katin bai yi ba, sai ya ba ta abin ta. Dawowar ta gida ke da wuya sai kawai ta ga saƙo daga bankin ta, cewa ta cire N30,00. A lokacin ne ta duba katin da ke hannun ta, sai ta ga ashe wani daban Abdullahi ya ba ta, ba na ta na ainihi ba. 

A lokacin da Abdullahi ke amsa tambayin jami'an tsaro, ya bayyana cewa 'takanas ta Kano' tun daga Kano ya je Bauchi don rinƙa yin wannan aiki na canja wa mutane katin su na ATM, ya ce yana yin haka ne don tara kuɗin aure. 

Mai lafin ya ce, shi da kansa ne ya samu wannan dabarar. Ya ce duk katunan ATM biyar da aka samu a wurin sa, na mutanen da ya damfara ne. 

 

No comments