Daga Muhammad Awwal, Minna Mai ba Gwamnan jihar Neja shawara kan harkokin siyasa da tsare-tsare, Hon. Muhammad Nma Kolo ( Jawon Minna) ya ba...
Daga Muhammad Awwal, Minna
Mai ba Gwamnan jihar Neja shawara kan harkokin siyasa da tsare-tsare, Hon. Muhammad Nma Kolo ( Jawon Minna) ya bayyana cewar amincewar Majalisar Dokokin jiha kan kasafin kuɗin da manomi Gwamna, Hon. Umar Bago ya gabatar wa Majalisar, har ta kai ga amincewar Majalisar tare da sanya masa hannu, akwai ƙwarin gwiwar kasafin zai fitar da kitse a wuta.
Ya ce, "Domin wannan ya nuna cewar Majalisar Dokokin da Majalisar zartarwa, duk ƙudurin su ɗaya na kawo ci gaba a jihar nan."
Ya ƙara da cew, Gwamna na da ƙwarin gwiwa wajen ayyukan raya pasa da ya shafi hanyoyi da wasu muhimman ayyuka da zai bai wa masu aniyar zuwa jihar don zuba jari a fannoni da dama amincewa da gayyatar da ya yi masu na haɓɓaka tattalin arzikin jihar.
Ɗan siyasar ya ci gaba da cewar, dangane da bada muƙaman siyasa a cikin gwamnati kuwa, Gwamnan ya taka rawar gani sosai, amma ba kowa ne zai samu muƙamin siyasa ba.
Ya ƙara da cewa, Gwamnan ya ga dacewar dawo da martabar noma, kan haka ya sa ya mayar da hankali a ɓangaren noma, domin ya riga ya sayar da jihar ga manyan manoma ta yadda jihar Neja ta zamo ta ɗaya da ake rububin shigowa don haɓɓaka harkar noma.
"Ina da yaƙinin nan gaba kaɗan, idan ka kira matashi don ka ba shi muoamin siyasa, ba zai saurare ka ba, saboda tallafin da ake son baiwa masu ƙananan sana'o'i ta yadda za su dogara da kan su.
"Muna da yalwar ƙasar noma da kiwo, muna da abubuwan sarrafawa da za a kai kasuwa. Yanzu haka akwai 'yan kasuwar ƙasashen waje da suka kawo shawarar noma, wasu muhimman abubuwa da duniya ke ya yi, wanda yalwar ƙasar da faɗinta zai ba mu damar cin gajiya ko moriyar arzikin da ke lulluɓe a pasa, wanda lungu da saƙo, gwamnati ta ɓullo da shirin gyaran hanyoyi don kai wa gare su."
No comments