Daga Awwal Umar, Minna Tsohon Sanata mai wakiltar Mazaɓar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewar lokacin da yake Majalisar Da...
Daga Awwal Umar, Minna
Tsohon Sanata mai wakiltar Mazaɓar Kaduna ta Tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewar lokacin da yake Majalisar Dattijai ya hana Tsoshon Gwamna ElRufa'i ciwo bashin Dalilolin Miliyoyin Naira don tsoron halin da jihar za ta samu kan ta, wanda a yanzu gwamnatin da ta gaje shi ta ke fuskanta.
Sanatan ya bayyana hakan ne a wata hirar musamman da ya yi da kafar sadarwa ta Achaza online TV, inda ya bayyana cewa, yanzu bashin da ake bin jihar Kaduna ya kai sama da Dala Miliyan Ɗari Shida, wanda a lokacin an karɓo su ne akan kowace Dala tana a kan Naira Ɗari Uku da Hansin, yanzu kuwa Dala ta kai Naira Dubu Ɗaya da ɗoriya, kuma tilas ne a ci gaba da zaftare bashin nan a cikin kason da gwamnatin tarayya ke bai wa jihohin Ƙasar nan.
"Yanzu ruwan bashin da jihar ke biya ya nunka kashi uku na abin da aka karɓo, kuma ba wani aikin kirki da gwamnatin El-Rufa'i ta yi wa jihar da kuɗaɗen.
"Duk wani abin da ka gani a jihar Kaduna, na El-Rufai ne da 'yan uwans. A lokacin mutane sun jahilci manufar mu, amma yanzu da suke ji a jikinsu sun fahimci dalilan mu na hana ciwo wannan bashin', in ji Sanata Sani.
Sanatan ya ce, "maganar na yi takara na faɗi, wannan al'ada ce ta siyasa, duk ɗan siyasa faɗuwa zaɓe bai tayar mai da hankal. Na yi takara 2013, ban ci ba, kuma gwiwa ta ba ta yi sanyi ba. Na sake gwadawa, na faɗi, amma da lokaci ya yi, na tafi zauren Majalisar Dattijai tsawon shekaru hutu, na dawo na jaraba takarar kujerar Gwamna, ban samu nassra ba, idan lokaci ya yi 2027, da yardar Allah zan sake gwada takarar."
Ya ƙara da cewa, "Da yawan 'yan siyasar mu a yau sun tafi siyasa ne don neman kuɗi, shi ya sa har su kammala riƙe muƙaman siyasa, ba wani abin a zo a gani da za su aiwatar."
"Tun farko mu ne muka yi gwagwarmayar dawo da mulkin Dimokuraɗiyya a ƙasar nan, wanda Marigayi Sani Abacha ya kai ni fursuna tsawon shekaru huɗu, yau mu na gode wa Allah mulkin Dimokraɗiyya ya zauna a pasar nan, kuma manufar mu ta siyasa tana nan daram, ba abin da ya canja."
No comments