Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Emefiele: Hukumar EFCC Za Ta Ɗaukaka Ƙarar Tarar Da Kotu Ta Yanke A Kan Ta

Daga Musa Muhammad  Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa ta EFCC ta nuna rashin amincewar ta da hukuncin da wata babbar kotu a A...

Daga Musa Muhammad 

Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa ta EFCC ta nuna rashin amincewar ta da hukuncin da wata babbar kotu a Abuja, inda ta yanke cewa Hukumar za ta biya Tsohon Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele Naira Miliya 100 bisa laifin keta masa haddi da Hukumar ta yi. 

Cikin wata sanarwa da Shugaban sashen hulɗa da jama'a na Hukumar, Dele Oyewale ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa, "a ranar Litini 8 ga watan Janairun 2024, Mai Shari'a O.A. Adeniyi ya ci tarar Hukumar EFCC ɗin ne bisa tsare Tsohon Gwamnan Babban Bankin, a lokacin da ta ke binciken sa, wanda kotun ta ce an tozarta 'yancin sa. 

Hukumar ta ce, an yanke wannan hukunci ne ba tare da la'akari da cewa an tsare Tsohon Gwamnan Babban Bankin ne bisa umurnin kotu ba. Don haka ta ce,  za ta ɗaukaka ƙara zuwa kotun ɗaukaka ƙara don a dakatar da hukuncin. 

 

No comments