Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Kogi Mai Barin Gado, Yahaya Bello, Ya Yi Sabbin Sauye-sauye A Jihar

* Ya tuɓe rawanin sarakuna uku, ya dakatar da ɗaya Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya rusa majalisar kwamishinonin sa tare da naɗa wata sa...



* Ya tuɓe rawanin sarakuna uku, ya dakatar da ɗaya

Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya rusa majalisar kwamishinonin sa tare da naɗa wata sabuwa a wani ɓangare na shirin miƙa mulki ga gwamnati mai jiran gado a jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa zaɓaɓɓen gwamnan Kogi, Alhaji Usman Ododo zai karɓi ragamar mulkin Bello a ranar 27 ga watan Janairu.

Waɗanda rushewar ta shafa sun haɗa da; Shuwagabannin hukumomi, jami’an tsaro da sauran waɗanda aka naɗa, duk da cewa an sake naɗa wasu daga cikinsu tare da sabbin mambobin majalisar.

A ɗaya ɓangaren kuma, Yahaya Bello ya tuɓe rawanin sarakunan gargjiya uku a jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa na jihar da aka yi a birnin Lokoja, ranar Lahadi.

A cewar gwamnan, matakin ya zo ne bayan bin duka dokoki da ƙa'idojin da suka shafi masarautun gargajiya kuma hakan na faruwa ne ƙasa da mako uku kafin ya sauka daga kan kujerarsa a matsayin gwamnan jihar.

Sarakunan gargajiyar da matakin ya shafa sun haɗa da Mai Martaba Alhaji Abdulrazaq Koto, Ohimege-Igu na Koton-Ƙarfe wanda kuma shi ne shugaban majalisar sarakunan gargajiya a ƙaramar hukumar Lokoja/Kogi. A yanzu za a mayar da shi ƙaramar hukumar Rijau ta jihar Neja, da zama.

Sai Mai Martaba Sam Bola Ojoa, Olu Magongo na Magongo wanda zai a mayar garin Salka a ƙaramar hukumar Magama da ke jihar Neja.

Mai Martaba Sarki Samuel Ayi Onimisi, Obobanyi na Emani wanda shi kuma za a mayar da shi garin Doko a ƙaramar hukumar Lavun da ke jihar Neja.

Game da tsige Onimisi, gwamna Bello ya ce muƙamin Obobanyi na Ihima da aka ɗaga darajarsa zuwa ta daya, "an yi haka ne ba tare da duba cewa mukamin Obobanyi na Ihima

Gwamnan ya kuma ce an dakatar da mai martaba Boniface Musa, Onu-Ife a ƙaramar hukumar Omala har sai yadda hali ya yi.

An kuma naɗa Ahmed Anaje, wanda shi ne Ohi na Okenwe a matsayin Ohinoyi na Ebiraland.

"Ibrahim Gambo Kabir kuma an naɗa shi a matsayin Maigari na Lokoja sai Dauda Isah da aka naɗa a matsayin Maiyaƙi na Kupa.

No comments