Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Zamfara Ya Yi Alķawarin Aiwatar Da Cikakken Kasafin Kuďin 2024

Daga Musa Muhammad  Gwamna Dauda Lawal ya yi alƙawarin aiwatar da cikakken ayyukan kasafin kuɗin 'ceto' na gwamnatin sa a 2024. A ra...

Daga Musa Muhammad 

Gwamna Dauda Lawal ya yi alƙawarin aiwatar da cikakken ayyukan kasafin kuɗin 'ceto' na gwamnatin sa a 2024.

A ranar Litinin ne Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya jagoranci taron Majalisar Zartarwar Jihar, wanda ya gudana a zauren majalisar a gidan gwamnati da ke Gusau.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa majalisar ta tattauna muhimman batutuwa da suka haɗa da kasafin kuɗin shekarar 2024.

 

A cewarsa, Gwamna Lawal ya kafa tsare-tsare da ayyukan gwamnatin sa na shekarar 2024.

Da yake jawabi ga majalisar, Gwamna Lawal, ya jaddada zai yi amfani da ingantattun tsare-tsaren da ke kunshe cikin kasafin na 2024 mai taken ‘Kasafin Ceto’ domin cimma nasara.

Ya ce, “Idan muka waiwaya baya, yana da muhimmanci mu yi godiya da irin nasarorin da wannan gwamnati ta samu duk da kalubalen tattalin arziki da walwalar rayuwa.

“A gaskiya, ƙoƙarinmu ya haifar da sabuwar ajanda ga sha’anin shugabanci a jihar. Labarin Jihar Zamfara ya canza a tsakanin watanni bakwai da suka gabata, kuma jihar na samun cigaba a daukacin bangarori,” inji Lawal.

Ya ƙara da cewa, a lokacin da suka kama mulki ran 29 ga Mayun 2023, sun ayyana muhimman bangarori tare da da ba da muhimmanci wajen magance matsalolin da suka fi addabar al’ummar jihar.

Kazalika, ya ce gwamnatinsa ta samar da shirye-shirye da da tsare-tsare masu inganci domin cimma manufar kasafin 2024 a fadin jihar

 

No comments