Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Zamfara Ya Raba Kayan Noma Ga Manoma A Tsafe

Gwamna Dauda Lawal ya miƙa wa manoman Zamfara da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe kayayyakin noma da muhimman iri na shuka. An gudanar da bikin rabo...

Gwamna Dauda Lawal ya miƙa wa manoman Zamfara da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe kayayyakin noma da muhimman iri na shuka.

An gudanar da bikin rabon kayan ne a ranar Litinin a sakatariyar Ƙaramar Hukumar Tsafe a wani ɓangare na cigaba da shirin farfaɗo da tattalin arziki da annobar na COVID-19 ya durƙusar wanda FADAMA III ta ɗauki nauyi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta bayyana cewa gwamnatin jihar Zamfara ta yi tanadi a cikin kasafin kuɗin shekarar 2024 domin gyara madatsun ruwa guda tara a ƙaramar hukumar Tsafe.

A cewarsa, yayin da yake jagorantar rabon kayan noman, gwamna Lawal ya jaddada ƙudirinsa na samar da ayyukan yi ga manoma sama da 40,000 a laramar hukumar.

A yayin jawabin nasa, gwamnan ya jaddada cewa madatsar ruwa ta Yanwaren Daji za ta taka muhimmiyar rawa wajen ciyar da mutane sama da miliyan biyu a duk shekara. “Tsarin samar da magudanar ruwa mai zai tabbatar da samun ruwa mai tsafta ga ɗaukacin ƙaramar hukumar Tsafe.

“Noma, wanda yake ɗaukar kashi 70% wajen haɓakar tattalin arziki, ya kasance ƙashin bayan tattalin arzikinmu. Bisa la'akari da haka, shirin namu ya shirya don bai wa manoma 100,000 a faɗin ƙananan hukumomin 14 kayan aikin noma da iri masu muhimmanci a cikin shekaru huɗu masu zuwa.

“Karamar Hukumar Tsafe ta shahara wajen noma da kuma gagarumar gudunmawar da ta ke bayarwa ga cigaban tattalin arzikin Jihar Zamfara. Tare da ƙaddamar da wannan shiri a wannan ƙaramar hukumar a yau, muna samar da damarmaki masu yawa ga al’ummomin da suke noma a wannan ƙaramar hukumar mai himma. Ina da yaƙinin cewa wannan shiri zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa noma, ta yadda za a kawar da talauci a yankunan karkara da ƙalubalen da ke tattare da shi.

“Daga wannan cigaba, muna shirin ɓullo da irin waɗannan ayyuka na shiga tsakani, kamar hadaddiyar shirin hada-hadar kasuwanci a Garin Magazu. Wannan shirin zai ƙunshi ayyuka daban-daban na haɗin gwiwar noma, waɗanda suka hada da kiwon kifaye, kiwon kaji da dai sauran su. Bugu da ƙari, zai ba da horo ga ƙananan 'yan kasuwa a sassa da yawa, zau kuma ba da gudunmawa sosai ga yunƙurin haɓaka tattalin arzikinmu.

"Bugu da ƙari, aikin zai taimaka wajen yaƙar cutar zazzaɓin cizon sauro ta hanyar sabbin hanyoyi kamar kiwon kifin 'tilapia' tare da samar da kuɗi mai yawa ga masu cin gajiyar ta hanyoyi daban-daban."

 

No comments