Daga Musa Muhammad A halin da ake ciki dai Gwamnonin jihohi huɗu ne suka dira harabar kotun ƙolin ƙasar nan da ke Abuja, inda a yau za a ya...
Daga Musa Muhammad
A halin da ake ciki dai Gwamnonin jihohi huɗu ne suka dira harabar kotun ƙolin ƙasar nan da ke Abuja, inda a yau za a yanke hukuncin kan makomar wasu Gwamnonin da suka ɗaukaka ƙarar dakatar da au da aka yi.
Gwamnonin, sun haɗa da Gwamna Dauda Lawal na Zamfara, Bala Muhammad na Bauchi, Abba Kabir Yusuf na Kano da Caleb Muftwamg na jihar Filato, akwai kuma Tsohon Gwamnan jihar Filato, Sanata Simon Lalong.
A hukuncin da za a yanke na yau ɗin, ya shafi Gwamnonin jihohin Kano, Bauchi Legas, Filato Abia, Ebonyi, Zamfara da Cross Rivers.
A yanzu haka kuma har kotun ta yanke hukunci kan na Legas, inda ta tabbatar da zaɓen Babajide Sanwo-Olu a matsayin Gwamnan Jihar.
Mai shari’a Garba Lawal, wanda ya yanke hukuncin ya yi watsi da ƙarar da Mista Rhodes-Vivour ya shigar.
No comments