Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Ɗaruruwan Musulmi Suka Ziyarci Kiristoci Don Bikin Kirsimeti

Daga Musa Muhammad  A wani abu da ya yi kama da neman hanyar samun zaman lafiya a tsakanin mabambantan addini, wasu musulmi sun ziyarar abok...

Daga Musa Muhammad 

A wani abu da ya yi kama da neman hanyar samun zaman lafiya a tsakanin mabambantan addini, wasu musulmi sun ziyarar abokan zaman mu Kiristoci har Cocin su domin taya su murnar zagayowar ranar kirsimeti ta bana a Kaduna. 

Musulman, waɗanda suka kasance masu yawa sun ziyarci wani Coci ne mai 'Christ Evangelical and Life Intervention Ministry' da ke Unguwar Gbagi Villa, Sabon Tasha, Kaduna, inda aka gabatar da jawabai na haɗin kai bisa koyarwar Yesu Almasihu. 

Cikin jawabin sa, babban Malamin Cocin, Pasto Dr. Yohanna Buru ya nuna matuƙar farin cikin sa bisa wannan ziyara da musulmin suka kai masu, inda ya ce, irin wannan ziyara za ta toshe duk wata kafar da maƙiya za su ɓullo don haddasa fitina da gaba. 

Ya ce, duk da hali na hunturu, rashin kuɗi, matsalolin tsaro da tsawwaluwar kuɗin mota bai hana musulmi maza da mata da ƙannan yara yin takakka daga jihohi daban-daban na Arewacin kasar nan don kawo wannan ziyara ba. 

Ya ƙara da cewa, wannan al'ada ta irin wannan ziyara, tana nuni da suna ƙauna da fahimtar addinan juna. 

Ya ce, musulmI ne daga ɓangarorin Tijjaniyya, Ƙadiriyya, Shi'a da sauran Ahlul Sunna suka kawo wannan ziyara, tare da miƙa kyaututtuka ga Cocin, wanda hakan ke nuna an kama hanyar samar da zaman lafiya da fahimta juna a addinance. 

Pasto Buru ya ce, sun kwashe shekaru 12 ke nan suna karɓar baƙuncin musulmi a duk lokutan bukukuwan Kirsimeti a wannan Coci. 

Shi kuwa cikin nasa jawabin, Shaikh Ibrahim Musa daga Hayin Kogi da ke Ƙaramar Hukumar Igabi a jjhar Kadna, ya nuna matuƙar farin cikin sa da jin daɗi ne bisa irin tarbar da aka yi masu a wannan ziyara da suka kai. 

Ya ce, shi ya ya ke ɗaukar musulmi da kirista duk ɗaya ne a zaman su na mutane, waɗanda ya kamata su tausaya wa juna. 

Daga nan sai Shaikh Musa ya yaba wa Pasto Buru bisa jajicewar sa wajen ganin an samu haɗin kai da zama lafiya a tsakanin mabbantan addiinai. 

 

No comments