Daga Hussaini Yero A ƙoƙarin da Sanata Abdulaziz Yari ke yi na ganin rage wahalhalun da al’ummar jihar Zamfara ke fuskanta sakamakon cire ta...
Daga Hussaini Yero
A ƙoƙarin da Sanata Abdulaziz Yari ke yi na ganin rage wahalhalun da al’ummar jihar Zamfara ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur, ya ƙara yawan mutanen da za su amfana da tallafin Azum, daga mutam 170,000 zuwa 250,000 a faɗin Jihar.
Sanata Abdulaziz ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga magoya bayan sa a gidan sa da ke Ƙaramar hukumar Talata-Mafara a makon da ya gabata.
Sanatan ya ce, zai ci gaba da bayar da muhimmanci wajen tallafa ma jama’a, musamman bisa la'akari da irin wahalhalun da ƙasar nan ke fama da su sakamakon firgicin ‘yan bindiga da cire tallafin man fetur.
Sai dai Sanata Yari ya yarda cewa, galibin matsalolin da ake fama da su a kasar nan na faruwa ne sakamakon laifuka ga Allah da mutane ke yi a kullum, yana mai kira da a tuba ga Allah.
Ya ce, tuba da addu’o’i ne kawai za su iya kawo ƙarshen matsalolin da ake fuskanta a ƙasar nan, musamman farmakin 'yan bindiga.
Ya ci gaba da cewa, gwamnatoci a dukkan matakai sun yi iya bakin ƙoƙarin su wajen ganin an kawo ƙarshen ta’addanci a ƙasar nan, amma abin ya ci tura.
Don haka ya buƙaci ɗaukacin ‘yan Nijeriya da su koma ga Allah da addu’o’in neman taimakon Sa a kan matsalolin da suka addabe mu.
Sanata Yari ya kuma koka da cewa, duk hanyoyin da za a bi wajen kawo ƙarshen ‘yan bindiga da makami, ko dai ta hanyar amfani da ƙarrfi ko tattaunawa a gwamnatance, amma duk da haka lamarin na ƙara taɓarɓarewa.
Ya kuma koka da irin mawuyacin halin da jama’a ke fuskanta a halin yanzu, wanda ya haifar da ƙarancin abinci ta yadda mutane da yawa suka kasa samun abinci sau biyu a rana.
No comments