Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Rikicin Haƙar Ma'danai Na Chanchaga Bai Shafi 'Yan Ƙungiyar Mu Ba - Nasko

Daga Muhammad Awwa, Minna Sakamakon rikicin matasan Kamfani da Chanchaga, wanda ya kai ga cin rayuwar mutum ɗaya a yammacin wata Alhamis a g...

Daga Muhammad Awwa, Minna

Sakamakon rikicin matasan Kamfani da Chanchaga, wanda ya kai ga cin rayuwar mutum ɗaya a yammacin wata Alhamis a garin Mina ta Karamar Hukumar Chanchaga da ke jihar Neja, Ƙungiyar leburori masu haƙar ma'adanai ( Nigeria Union Of Mine Workers) ta nesanta kan ta da rikicin. 

Shugaban Ƙungiyar a jihar Neja, Kwamared Musa Adamu Nasko ne ya bayyana haka, inda ya ce tun bayan da gwamnatin jiha ta shelanta dakatar da haƙar ma'adanai a jihar ta shawarcin mambobin su, su ka bi umurnin gwamnati.

"Don haka duk wani ɗan ma'adanai, in dai mamban mu ne da muka tantance kuma muka ba shi katin shaidar zama ɗan ƙungiya, har yanzu a zaune yake.

"Don haka wannan rigimar da ka ga matasan nan na yi, a tsakanin su ne, bai shafi mu 'yan ma'adanai na haƙiƙa ba. Rigima ce suka yi ta gaba a tsakaninsu. Yanzu muna ci gaba da yawatawa lungu da saƙo na jihar nan don ƙara wayar da kan 'ya'yan ƙungiya na haƙiƙa. 

"Saboda haka ina kira ga jama'a da su sani, waɗannan matasan da ake alaƙanta mu da su, kuskure ne babba, domin ba 'ya'yan ƙungiyar mu ba ne kuma ba mu da nasaba da su, domin mu masu biyayya ne ga gwamnati. Shi ya sa tun shelanta dakatar da haƙar ma'adanai a jihar nan muka miƙa wuya ga umurnin gwamnati.

"Don haka na ke kira da babbar murya, da cewar duk wanda jami'an tsaro suka cafke, to a tabbatar an miƙa shi gaban Ƙuliya. Kuma jami'an tsaro su ƙara ƙaimi wajen ganin an kawo ƙarshen wannan gabar matasan, domin ba abin da yake haifarwa face koma-baya da ruruta wutar rikici a cikin al'umma."

 

No comments