Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Magidanta 340 Ne Suka Sha Dukan Tsiya A Hannun Matan Su Na Aure A Legas

Daga Musa Muhammad  Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa ƙididdiga ta nuna tsakanin watan Satumba na shekarar 2022 da watan Yuli na 2023, a...

Daga Musa Muhammad 

Gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa ƙididdiga ta nuna tsakanin watan Satumba na shekarar 2022 da watan Yuli na 2023, aƙalla an samu ƙararraki na mazaje magidanta kimamin 340, waɗanda matan su na aure suka nakaɗa masu dukan tsiya. 

Shugabar Hukumar kula da rigingimun aure da cin zarafi ta jihar Legas DSVA, Titilola Vivour-Adeniyi ce ta sanar da haka ga kafar yaɗa labarai ta PM News. 

Vivour-Adeniyi ta ƙara da cewa wannan adadi na 340 ya nunka fiye da sau biyu a kan ƙararrakin da aka samu tsakanin Satumbar 2021 da Yulin 2022, wanda aka samu ƙararraki 140. 

Ta ce, wannan ya yi nuni ke nan da cewa maza na ƙara samun ƙwarin gwiwar fitowa su yi bayanin irin cin zafarin da matan su ke yi masu a cikin gida, na duka ko hana su jima'i. 

Sannan kuma abin ya na nuni da cewa ana ƙara samun yawan mazan da ke shan kashi a hannun matayen su. 

A halin da ake ciki dai gwamnatin jihar Legas ɗin ta fara wallafa sunayen mata ko mazan da ke cin zarafin abokin zaman sa, musamman ta fannin ƙaurace wa jima'i. 

A wani taron manema labarai da ta gabatar, shugabar Hukumar ta DSVA ta bayyana cewa fara wannan wallafa sunayen ya zo daidai ne da dokar da ta kafa Hukumar. 

Ta ce, duk mata ko mijin da aka kama da laifin ƙin amince wa juna ta jima'i, za a wallafa sunan sa da hoto da kuma irin laifin da ya aikara, ko ta aikata, "za kuma a bayyana yanayin hukuncin da kotu ta yanke masa," in ji Vivour-Adeniyi. 

In dai ba a manta ba, a kwanakin baya wannan jarida ta Matattarar Labarai ta kawo wani labarin mai kama da wannan, inda wani ya kai ƙara kotu kan irin ɗan karen dukan da ya ke Sha a hannun matar sa, inda ya nemi a taimake shi a raba auren. 

No comments