Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Me Ya Sa Ƙasar Nijar Ta Yanke Hulɗa Da Kasashe Masu Amfani Da Harshen Faransanci?

Daga Musa Muhammad  Gwamnatin Soja ta Ƙasar Jamhuriyar Nijar ta yanke duk wata hulɗa da Ƙungiyar ƙasashe masu amfani da harshen Faransanci (...

Daga Musa Muhammad 

Gwamnatin Soja ta Ƙasar Jamhuriyar Nijar ta yanke duk wata hulɗa da Ƙungiyar ƙasashe masu amfani da harshen Faransanci (OIF).

Gwamnatin Sojin ta yi zargin cewa Ƙungiyar mai mambobi 88, ƙasar Faransa na amfani da ita a matsayin makami don kare muradun Faransar. 

Wannan zargi ya fito fili ne yayin da mai magana da yawun gwamnatin Nijar ɗin ya furta haka a wani jawabi da ya gabatar a gidan talabijin na ƙasar a kwanakin baya. 

In dai za a iya tuanwa, a ranar 26 ga watan Yuli ne sojoji suka ƙwace mulki a Nijar, lamarin da Faransa da sauran ƙawayenta na Yammacin Duniya suka yi Allah-wadai da shi.

Nan da nan kuma gwamnatin mulkin sojin ta kori dakarun Faransa daga ƙasar, bayan shafe kusan shekara 10 da sunan yaƙi da ‘yan tada da sauran masu tayar da ƙayar baya a yankin.

Ƙungiyar ta OIF ta sanar da dakatar da mafi yawan ayyukan haɗin gwiwarta da Nijar a makon da ya gabata saboda juyin mulkin, amma ta ce za ta ci gaba da aiwatar da wasu ayyukanta da kai tsaye suke shafar al'umma, da kuma masu ƙoƙarin ganin an dawo da Dimokraɗiyya.

 

No comments