A ranar Asabar da ta gabata ne Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin Jihar na shekarar 2024 na Naira Biliya...
A ranar Asabar da ta gabata ne Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya rattaba hannu kan kasafin kuɗin Jihar na shekarar 2024 na Naira Biliyan 426.
Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta amince da kasafin kuɗin na Naira Biliyan 426,563,671,000.00 a matsayin ‘kasafin ceto’ a ranar Juma’ar da ta gabata.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce ƙiyasin shekerar 2024 ya kai Naira 118,358,079,515.00 (27%) da aka ware domin ayyukan yau da kullum, da kuma Naira 308,205,591,485.00 (73%) na manyan ayyuka.
Ya Ƙara da cewa, kasafin, wanda ke da taken 'kasafin kuɗin ceto' zai ƙara haɓɓaka zuba jari a cikin gida da waje, da samar da ayyukan yi, da sauƙaƙa harkar kasuwanci a jihar Zamfara.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Ƙudirin kasafin 2024 da Gwamna Lawal ya sanya wa hannu ya ba da fifiko ne ga ɓangarori shida masu muhimmanci ga ci gaban jihar Zamfara: tsaro, ilimi, noma, lafiya, samar da ababen more rayuwa, da sauran su.
“Ƙudirin yana da kiyasin kamar haka: Ayyukan mulki - N72,093,326,763 (17%); Ɓangaren Tattalin Arziki – N244,729,584,729 (57%); Ɓangaren kyautata jin daɗin jama'a – N103,139,659,508 (24%); sannan harkar Shari'a - N6,601,100,000 (2%).
“Bugu da ƙari, kasafin 2024 da aka amince da shi ya yi ƙiyasi a kan sassa: Noma - N38,144,000,000; Ilimi - N51,370,787,508; Lafiya - N33,922,370,000; da ababen more rayuwa da raya birane - Naira Biliyan 109.
Kasafin ya ware isassun kuɗaɗe ga shirye-shiryen inganta rayuwar jama'a, don sauƙaƙa masu game da halin matsin tattalin arzikin da ke ciki, da kuma harkar tsaro.
“Waɗannan shirye-shiryen sun haɗa da ba da rancen kuɗi kaɗan ga ƙanana da matsakaitan masana'antu, shirin FADAMA don samar da abinci, da sauran tsare-tsare na rage talauci. Za kuma a mu ƙarfafa shirye-shiryen mu na Samar da Fasaha don samar da guraben ayyukan yi ga ɗimbin al’ummarmu a Jiha.
“Kuɗin kasafin kufin da aka amince da shi ya yi daidai da dogon hangen nesa da tsare-tsare na Gwamna Lawal. Yana jaddada ayyukan da suka yi daidai da burin ’yan jihar, da kuma wasu shirye-shiryen da za su yi tasiri kai tsaye ga burin mutanen mu.
No comments