Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Zamfara Ta Sasanta Rikicin Masallacin Da Ya Shekara 7 A Rufe

Daga Musa Muhammad  Gwamna Dauda Lawal ya sasanta rikicin shekara bakwai (7) da ya kai ga rufe ɗaya daga cikin manyan masallatan Juma’a na g...

Daga Musa Muhammad 

Gwamna Dauda Lawal ya sasanta rikicin shekara bakwai (7) da ya kai ga rufe ɗaya daga cikin manyan masallatan Juma’a na garin Moriki da ke ƙaramar hukumar Zurmi.

An rufe masallacin Juma'ar na Moriki sama da shekaru bakwai (7) sakamakon taƙaddamar da ta ɓarke tsakanin ɓangarori biyu na al'ummar yankin.

 A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar yau, ya ce ɗaukar matakin ya zama dole domin magance matsalar rashin haɗin kan jama’a.

A cewarsa, gwamnan ya lura da muhimmiyar rawar da haɗin kai ke takawa wajen samar da zaman lafiya da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa, musamman a mawuyatan lokuta.

“A jiya ne Gwamnatin jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal ta warware rikicin shekara bakwai (7) da ya yi sanadiyar rufe ɗaya daga cikin manyan masallatan Juma’a na garin Moriki dake ƙaramar hukumar Zurmi.

“Gwamnatin jihar Zamfara ta ga ya dace ta shiga tsakani tare da ɗaukar matakan daƙile duk wani abu da ke kawo rashin haɗin kai a tsakanin al’umma.

“Gwamna Lawal ya umurci ma’aikatar kula da harkokin addini da ta gina sabon masallaci ga ɗayan ɓangaren masu jayayya. Ana sa ran kammala sabon masallacin nan da watanni uku (3).

“Dukkan ɓangarorin biyu (2) sun amince su bi ƙa’idojin yarjejeniyar gwamnati.

An yi sallar Juma'a jiya a masallacin ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Moriki, wanda ya gabatar da huɗuba a kan haɗin kai tsakanin al'umma.

A nasa jawabin, Sarkin Moriki, Bashar Isma’ila Muhammad, ya miƙa godiyarsa ga Allah da ya nuna masa ranar da wannan rikici ya kai ƙarshe. 

Sarkin kuma ya yaba wa gwamnatin jihar Zamfara akan ƙoĵarinta na sulhunta waɗannan ɓangarorai guda biyu na al'umma.

No comments