Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sanya hannu kan wata doka da ta haramta wa Sarakunan gargajiya bayar da takardar shaidar amincewa da h...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sanya hannu kan wata doka da ta haramta wa Sarakunan gargajiya bayar da takardar shaidar amincewa da haƙar ma’adanai a faɗin jihar.
A ranar Alhamis ne aka rattaba hannu kan dokar zartarwar a zauren majalisar gidan gwamnati da ke Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, an sanya hannu kan dokar harancin ne domin dakatar da ɗaya daga cikin munanan da ke ba da damar ayyukan ta'addanci.
A cewar sa, odar ta haramta duk wasu takardar neman izinin haƙar ma’adanai. "Wannan ya haɗa da takardar yarje wa mutane, kamfanoni, ko ƙungiyoyi don ayyukan haƙar ma'adinai."
A jawabin sa yayin da yake sanya hannu a kan wannan umarni, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa an yanke hukuncin ne saboda tsananin hatsarin da ke tattare da yawaitar amincewa da haƙar ma'adanai.
Ya ce, “A yau, a ƙudurin gwamnati na na magance matsalar rashin tsaro, na sanya hannu kan wata doka da ta haramta wa Sarakunan gargajiya bayar da takardar neman izinin haƙar ma’adanai a faɗin Ƙananan Hukumomi 14 na jihar Zamfara.
“Kamar yadda babban mai shari’a ya bayyana, an gano ayyukan haƙar ma’adanai a Zamfara a matsayin wani muhimmin al’amari da ke kawo taɓarɓarewar tsaro a jihar, musamman matsalar 'yan bindiga.
“A matsayin mu na gwamnati mai kulawa da al'ummar ta, yana da matuƙar muhimmanci mu ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki don magance matsalar haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da ke haifar da rikici.
"Shi ya sa na rattaba hannu kan dokar zartarwa. Muna ɗaukar duk matakan da suka dace don gyara matsalolin da ke tattare da ba da takardar yarda.
"Muna roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya shiryar da mu yayin da muke hidima da kuma kare rayuka da dukiyoyin mutanen jihar Zamfara."
No comments