Daga Musa Muhammad Dubban ɗaruruwan jama'a ne suka cika titunan garin Gusau ta jihar Zamfara don yi wa Gwamna Dauda Lawal lale marhabin...
Dubban ɗaruruwan jama'a ne suka cika titunan garin Gusau ta jihar Zamfara don yi wa Gwamna Dauda Lawal lale marhabin da dawowa daga Abuja, tare da taya juna murnar samun nasara a hukuncin da kotun ƙoli da ke Abuja ta yanke, inda ta tabbatar da sahihancin zaɓen da aka yi masa.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya bayyana cewa garin Gusau ya tsaya cik don muna murna da farin cikin wannan nasara da aka samu a kotun ƙolin.
Idris ya ce, Zamfarawa sun yi dafifi a titunan garin, inda suke ɗaɗɗaga hannayen su ga Gwamnan da tawagar sa a yayin da ya ke wucewa ta cikin garin, suna masu cikin farin ci da annashuwa.
Ya ce, Gwamnan ya fito da jikin sa ta saman wata mota da ake wa laƙabi da Bazamfara, ya na ɗaɗɗaga hannun, yana karɓar gaisuwa daga dubun-dubatar jama'a, a yayin da ya wuce ta Ƙaramar Hukumar Tsafe, Kwatarkwashi da Damba, a hanyar sa ta zuwa filin wasa na 'Freedom Square' da ke Gusau.“Wannan tafiya ta kai ta awanni 10, inda ta ko'ina aka ratsa, dubban mutane ne ke kiɗe-kiɗe da raye-raye, tare da ɗaɗɗaga alluna masu ɗauke da rubutun nuna jin daɗin nasarar da Allah ya ba Gwamna Lawal a kotun."
Cikin jawabin da ya gabatar ga dubun-dubatar jama'ar da ta taru a filin wasa na Freedom Square, Gwamnan, bayan da ya yi godiya ga Allah, ya yaba da sashen Shari'a da suka tsaya a kan gaskiya, duk da kuwa ƙalubalen da suka fuskanta.
“Ina matuƙar godiya ga sashen Shari'a, sannan kuma da gwamnatin tarayya, musamman na rashin tsoma bakin ta a harkar Shari'ar, musamman ƙararrakin zaɓe. Wanda wannan ya kawo wata fata ga ƙasar nan baki ɗaya.
Da ya juya game da Zamfarawan kuwa, Gwamna Lawal ya tabbatar masu da cewa harkar tsaro ne babban abin da ya sanya a gaba, kamar dai yadda ya yi alƙawari. “Mu na samun ci gaba wajen shawo kan matsalar nan, kuma za mu ci gaba da jan damtse. Mun yi namijin ƙoƙari wajen harkokin ilimi, lafiya, noma tattalin arziki da sauran muhimman fannoni na rayuwa.Daga ƙarshe Gwamna Lawal ya tuna baya, ya ce, “gwamnatin da ta gabata ta hana mu wuri don mu yi taron yaƙin neman zaɓe, duk da kuwa mun bi hanyoyin da suka wajaba a doka. Saboda haka sai muka zo wannan wurin muka yi taron yaƙin neman zaɓen mu. Don haka, sai muka yanke shawarar canja wa wannan wuri suna, zuwa Filin 'Yanci ('Freedom Square'.")
No comments