Wani ɗan kasuwa a Kaduna, mai suna Haruna Adamu ya nemi Alƙali ya sanya matar sa ta ba shi sadakin da ya kashe mata, ko kuma dole ta ci ga...
Wani ɗan kasuwa a Kaduna, mai suna Haruna Adamu ya nemi Alƙali ya sanya matar sa ta ba shi sadakin da ya kashe mata, ko kuma dole ta ci gaba da zama da shi matsayin matar sa.
Haruna Adamu, ya yi wannan roƙo ne lokacin da kai ƙarar matar tasa, Salamatu Abubakar a kotun Shari'a da ke Magajin Gari, Kaduna, in da ya nemi kotun ta tilasta mata.
Malam Adamu ya ce, bai damu ya rabu da ita ba, amma dai matsalar ita ce, shi ba shi kuɗin da zai ƙara yin wani auren.
Ya ce, “Saboda haka idan matar tawa ba ta son ta dawo wuri na, to ta dawo mani da sadakin da na biya mahaifan ta."
Ya ci gaba da bayyana wa kotun cewa, ya sami matar tasa a matsayin Bazawara, amma ya yanke shawarar ya aure ta. Ya ce, a cikin watanni takwas da suka yi da aure, watanni biyu na farkon auren nasu ne kawai ya yi su cikin jin daɗi.
Adamu ya ce wa Alƙalin, a watanni shida da ta yi a gidan su, ya na aika mata da kayan abin ci da kuɗi.
"Ina son mata ta, don haka ina so ta dawo gida na, amma in ba ta son dawowa, to ta biya ni sadakin da na ba iyayen ta, don in samu in yi wani auren. Ba ni da wasu Kuɗin yin wani auren."
A na ta ɓangaren, Malama Salamatu ta shaida wa kotun cewa, ta gudu daga gidan auren na ta ne saboda irin cin mutuncin da Adamu ke yi ma ta.
Ta ci gaba da cewa, maigidan nata ba ya tausaya wa halin da mahaifiyar ta ke ciki na rashin lafiya. Don haka, ta gwammace ta dawo masa da sakin sa na N75,000, wanda ya ba iyayen ta, a kan ta ci gaba da zama da shi.
Daga nan sai Alƙalin kotun, Malam Isiyaku Abdulrahman ya ɗage sauraron Shari'ar zuwa 17 ga wannan wata na Janairun 2024.
Yana mai cewa wannan zai ba da dama ga mai ƙarar ya kawo hujjojin sa na abubuwan da ya ce ya na aika mata, da kuma kuɗaɗen da ya ke aikawa.
No comments