Daga Imrana Abdullahi An bayyana hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke game da batun siyasa da zaɓen Jihar Zamfara a matsayin wata Ishara kasancew...
Daga Imrana Abdullahi
An bayyana hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke game da batun siyasa da zaɓen Jihar Zamfara a matsayin wata Ishara kasancewar mutane da dama ne suka taru a wuri guda amma kuma Allah maɗaukakin Sarki ya nuna ikonsa a kansu baki ɗaya don haka dukkan ’yan siyasa a Jihar Zamfara da kasa baki ɗaya lamarin ya zama Ishara a kansu.
Wani fitaccen ɗan siyasa daga Ƙaramar Hukumar Talatar Mafara a Jihar Zamfara Alhaji Bashir Nafaru ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da wakilinmu ta kafar sadarwar "Whatsapp", inda ya ci gaba da bayanin cewa dukkan ’yan siyasar Jihar Zamfara Allah ya tattara su duk da taron ƙangin nasu da suka yi a kansa ya Jefa su cikin kwandonsa don haka sai ayi haƙuri zuwa wasu ’yan shekaru da fatan Allah ya tabbatar da abin da ya fi zama alkairi.
Nafaru, ya kuma yi kira ga Gwamnan Jihar Zamfara da kotu ta tabbatar mashi cewa ya duba Jihar Zamfara na halin da ake ciki na rashin tsaro duk da cewa kowa ya san ana iyakar ƙoƙarinsa amma ya ƙara ƙaimi sosai
Bashir Nafaru, ya kuma ƙara da faɗakar da Gwamna Dauda Lawal da cewa ya ƙara ƙoƙari wajen zuwa ga Gwamnatin tarayya a amso dukkan abin da ya san haƙƙi ne na Jihar Zamfara ya kwato domin azo a raba wa matasa kasancewar matasan na buƙatar samun hanyoyin da za su samu abin yi, domin rashin abin yi ma na taimakawa wajen matsalar rashin tsaro don haka idan akwai abin yi za a samu sauki kwarai.
"Alhamdulillahi, ni da ba ɗan PDP ba amma duk da haka hukuncin Kotun Ƙoli dole ne a ce wata Ishara ce daga Allah madaukakin Sarki, duk wani da yake ji da kansa a Jihar Zamfara cewa shi dan siyasa ce duk Allah ya tattara su a cikin kwando guda ya kawo wani mutum daya ya ce shi ne don haka muna goyon bayansa, Allah ka tabbatar mana da alkairi ya sa a gama wannan mulkin nasa cikin kwanciyar hankali da lumana cikin hukuncin ubangiji.
No comments