Daga Musa Muhammad A ƙoƙarin da Gwamnatin Jihar Zamfara ke yi na ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaron da ya addabi Jihar, wanda sanadiyyar ...
Daga Musa Muhammad
A ƙoƙarin da Gwamnatin Jihar Zamfara ke yi na ganin an kawo ƙarshen matsalar tsaron da ya addabi Jihar, wanda sanadiyyar hakan ake samun naƙasu wajen Noma da gudanar da ɗaukacin harkokin rayuwa baki ɗaya, Gwamnatin ta kafa wasu jami'an samar da tsaro na musamman, inda ta gayyaci Tsohon Gwamnan jihar, kuma ƙaramin Ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle domin halartar bikin ƙaddamarwar, wanda za a gudanar a ranar 31 ga watan Janairu, 2024.
Kamar yadda wata sanarwar da ta fito daga shugaban ma'aikatan Gidan Gwamnatin Jiha, ta sanar da cewa Gwamna Dauda Lawal ya gayyaci Ministan ƙasa a ma'aikatar tsaro Muhammad Bello Matawalle a matsayin baƙo na musamman.
Sanarwar ta ce, "Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal ya gayyaci tsohon Gwamna Muhammad Bello Matawalle domin ya kasance a matsayin baƙo na musamman a wajen taron da za a yi domin yaye jami'an tsaron al'umma da Gwamnatin Jihar ta horar da ake kiran su da (Askarawa), "Community Protection Guards".
Kamar yadda wata sanarwar da ta fito daga shugaban kwamitin shirya taron Mouktar Lugga, taron da aka shirya za a yi shi ne a garin Gusau a ranar 31 ga watan Janairu, 2024, ana sa ran Gwamnoni shida ne za su halarci taron daga yankin Arewa maso Yamma, da kuma wakilai daga Gwamnatin tarayya da kuma jama'a a ciki da wajen Nijeriya.
Tun da daɗewa dai Gwamna Dokta Dauda Lawal na yin kira ga 'yan siyasa da su ajiye batun bambancin siyasa a gefe, kowa ya taho a haɗa hannu domin ciyar da Jihar gaba.
Ya ci gaba da bayanin cewa alƙawarin da ya yi na cewa zai yi aiki tare da kowa kuma a buɗe ta hanyar aiwatar da aiki tare da gaskiya da amana kamar yadda ya ɗauki alƙawari tun a lokacin da ya yi rantsuwar kama aiki.
Sauran waɗanda aka gayyata sun haɗa da dukkan tsofaffin Gwamnonin jihar, tsofaffin Mataimakan Gwamnonin Jihar, 'yan majalisun tarayya da na Jiha masu ci da tsofaffi da kuma tsofaffin 'yan majalisar zartarwar Jihar, Sarakunan gargajiya da kuma dukkan shugabannin jam'iyyun da ke jihar.
No comments