Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ƙungiyar Ci Gaban Kaduna Doka Ta Gudanar Da Taron Shekara

Daga Imrana Abdullahi Cikin 'yan kwanakin nan ne ƙungiyar ci gaban cikin garin Kaduna, Doka, Wato KADDA ta gudanar da taron ta na shekar...

Daga Imrana Abdullahi

Cikin 'yan kwanakin nan ne ƙungiyar ci gaban cikin garin Kaduna, Doka, Wato KADDA ta gudanar da taron ta na shekara-shekara, inda Shugaban ƙungiyar, Honorabul Sani Rabi'u Baƙo ya bayyana nasarorin da su ke samu da cewa wani al'amari ne daga Allah maɗaukakin Sarki.

Hon. Baƙo ya bayyana haka ne a lokacin da ya tattauna da manema labarai, jim kaɗan bayan kammala taron ƙungiyar na bana, inda aka gabatar da muhimman jawabai da kuma bayar da satifiket da lambobin karramawa na shekarar 2023.

Sani Rabi'u Bako, ya ci gaba da cewa duk da wannan Ƙungiyar ba ta siyasa ko samun kuɗi ba ce, amma dai ta na gabatar da muhimman ayyuka a ɓangarorin ciyar da al'umma gaba.

A nan ya kawo misalin wasu abubuwan da su ke aiwatarwa, waɗanda suka hada da taimaka wa Marayu, koya wa yara sana'o'i, koya wa matasa karatun dabarun yadda za su rubuta jarabawar NECO da WAEC da kuma JAMB da nufin samun manyan gobe masu ilimi da hazaƙa.

Ya ce kuma ƙungiyar na gabatar da aiki a kan samar da Zakka da raba wa mutanen da suka cancanci a ba su da suke a cikin jama'a.

"Ba ƙungiya ba ce ta cin riba ba, sai dai kawai ana yin ayyukan ne domin a taimaka wa jama'ar yankin mazaɓun Doka, Shaba, Gaji da Mazabar Liman duk a cikin yankin Ƙaramar Hukumar  Kaduna ta Arewa. 

"Muna kuma taimaka wa Mata masu buƙatar taimako da marayu ta hanyar sana'o'i da sauran su, da masu fitar da zakka a raba wa al'umma da ba su da hali. Muna kuma bi domin tabbatar da cewa akwai zaman lafiya a wannan yankin."

Da yake gabatar da ƙasida a wajen taron, Farfesa Kabiru Isah daga Jami'ar Ahmadu Bello Zariya, dogon jawabi ya yi a kan muhimmancin ilimi da kuma irin yadda ake samun ci gaba a wajen tafiyar da al'amuran duniya, musamman ta hanyar yin amfani da yanar Gizo.

Farfesa Kabiru ya yi kira ga ɗaukacin al'umma da su hanzarta rungumar hanyoyin samun ci gaba na zamani domin gudun kada a bar su a baya.

Shi kuma cikin tasa ƙasidar mai taken 'gudunmawar matasa wajen ci gaban al'umma', Dokta Aliyu Adamu Isah bayyana matasa ya yi da cewa mutane ne masu matuƙar muhimmanci a cikin al'umma.

Ya ce, "Matasa za su iya bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban ƙasa da al'umma baki ɗaya. 

"Kuma ya dace matashi ya zama mai dogaro da kansa a kodayaushe, ya kuma riƙa yin aiki da kula ta hanyar tabbatar da 'yan uwantaka tsakaninsa da juna, matashi ya riƙa danne zuciya a kodayaushe kafin gabatar da al'amura.

"Sai dai ya dace a riƙa ƙarfafa wa matasa domin ba su ƙwarin gwiwa, domin matasa na saurin yin gangamin tara sauran matasa 'yan uwansu a duk lokacin da wani abu ya faru.

"A rika sauraren matasa  a na shigo da su a cikin gudanar da harkoki na yau da kullum ta yadda za a riƙa Koyar da su a kodayaushe.

"Saboda a mafi yawan lokuta idan matashi ya ga karatu ko makaranta ba za su ba shi abin da yake buƙata ba, sai ya koma ya nemi wani abin daban da yake ganin zai ba shi abin da yake so, don haka sai an yi a hankali a kodayaushe."

Jama’a da dama ne dai suka gabatar da jawabai a wurin wannan taro da ya tara ɗimbin mutane. 

 

No comments