Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za A Ƙara Farashin Jaridu A Watan Janairu Mai Zuwa -NPAN

Daga Musa Muhammad  Ƙungiyar masu kamfanonin wallafa jaridu ta Nijeriya, wato 'The Newspaper Proprietors’  Association of Nigeria (NPAN)...

Daga Musa Muhammad 

Ƙungiyar masu kamfanonin wallafa jaridu ta Nijeriya, wato 'The Newspaper Proprietors’ 

Association of Nigeria (NPAN)' ta bayyana cewa daga ranar 2 ga watan Janairun 2024 sabon farashin jaridu zai fara aiki a duk faɗin ƙasar nan. 

Babban Sakatare na Ƙungiyar ta NPAN, Feyi Smith ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a Abuja cikiin makon da ya gabata. 

Mr Feyi ya ce, "Ƙungiyar mu da ɗauki wannan tsattsauran mataki ne bisa nazarin da ta yi na matsin tattalin arzikin da mambobin mu ke ciki, musamman na kayan buga jaridun."

Ya ƙara da cewa, tashin gwauron zabin da kayan aiki ke yi, sannan ga faɗuwar da darajar Naira ke yi, wanda ya sanya yanzu sam ba sa samun wata riba a harkokin nasu, musamman a waɗannan shekarun. 

Sai dai duk da tashi da hauhawar da kaya ke yi a shekarun nan, Mr Feyi ya bayyana cewa yau shekaru huɗu ke nan ba su yi ƙarin farashin jarida ba, duk da kuwa kuɗin kayan aiki sun nunka nunkin-banunkin. 

Daga nan shugaban mawallafa jaridun ya yi fatan cewa masu karatun jaridu za su fahimce su a wannan sabon farashin da za su sanya, su sani dole ce ta sa su yin wannan ƙari. 

Ya ce, "Muna fata masu karatun jaridu za su fahimci dalilan mu na yin wannan ƙari, musamman ganin cewa muna ƙoƙari wajen zamanantar da yanayin wallafa jaridun, don samun jaridu da rubutu masu inganci."

 

No comments