Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gobara Ta Laƙume Shaguna Na Miliyoyin Naira A Kano

’Yan kasuwa da dama sun yi asarar dukiya ta Miliyoyin Naira a wata gobara da ta ƙone shaguna da dama a garin Gwarzo da ke Karamar Hukumar Gw...



’Yan kasuwa da dama sun yi asarar dukiya ta Miliyoyin Naira a wata gobara da ta ƙone shaguna da dama a garin Gwarzo da ke Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano.

Lamarin gobarar ya auku ne a ranar Litinin ɗin da ta gabata, wanda luma ya jefa mutane cikin babbar asarar ta sanya aka ga yawancin su suna kuka.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano, Saminu Yusif Abdullahi, ya ce gobarar ta tashi ne da tsakar dare amma daga ƙarshe aka kashe da safiyar Litinin.

Ya bayyana cewa, gobarar ta ƙone shaguna da dama ƙurmus, yayin da ta lalata dukiya ta Miliyoyin Naira. Sai dai ya ce babu wani rauni ko asarar rai.

Ɗaya daga cikin ’yan kasuwar, Dayyabu Lawan Bala, ya ce ya yi asarar dukiya ta sama da Naira Miliyan 5 ciki har da shagon sa. Daga nan sai ya yi kira ga gwamnati da sauran masu hannu da shuni da su kawo musu ɗauki domin rage raɗaɗin da suke ciki.

Ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Gwarzo ta tarayya, Hon Abdulahi Muazu Babangandu ya jajanta wa ’yan kasuwar tare da bayar da gudunmawar Naira 500,000 bayan ya ziyarci wurin.

No comments