Wani matashi ɗan shekara 19 ya daɓa wa budurwar sa wuƙa ya hallaka ta a kan kuɗi Naira dubu biyar a Jihar Bauchi. Kakakin ’yan sandan jihar,...
Wani matashi ɗan shekara 19 ya daɓa wa budurwar sa wuƙa ya hallaka ta a kan kuɗi Naira dubu biyar a Jihar Bauchi.
Kakakin ’yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammad Wakil, ya bayyana cewa tuni ’yan sanda sun kama wanda ake zargin.
Wakil ya ce, “abin ya faru ne a lokacin da wanda aka kashe ɗin ta buƙaci a biya ta Naira 5000 da ta ke bin (wanda ake zargin) bashi, a kan harkokin da suka yi a baya.
“Ana cikin haka sai gardama mai zafi ta shiga tsakanin su har ta kai ga ya daɓa mata wuƙa, ta samu mummunan rauni wanda ya kai ga mutuwar ta.”
Wakil ya bayyana cewa a ranar 18 ga watan Disamba, 2023 jami’an tsaro suka kama shi a unguwar Sabon Layi Kano Road Bauchi bisa zargin kashe Emmanuella Ande.
A cewar sa , an kama shi ne sakamakon kiran da wani mutum ya yi musu cewa wanda ake zargin ya shiga ɗakin otal da ke Bayan Gari, ya daɓa wa budurwar sa wuƙa a ƙirji.
“Jama’a sun yi yunƙurin ceto ta, inda suka ɓalle ƙofar ɗakin, shi kuma ya daɓa wa wani Zaharaddeen Adamu wuƙa a hannun hagun sa,” in ji shi.
Wakil ya ce, ’yan sanda sun hanzarta kai ɗauki, inda suka yi ƙoƙarin ceto wacce aka kashen, aka kai ta asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Ɓalewa (ATBUTH) Bauchi inda likita ya tabbatar da rasuwar ta, kuma aka ajiye gawar a ɗakin ajiyar gawa.
Hakazalika, an kai Zaharadeen an yi masa magani a asibitin ’yan sanda, aka sallame shi, wanda ake zargin kuma a halin yanzu ana ci gaba da bincike.
No comments