Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bikin Kirsimeti; 'Yan Uwa Musulmi Sun Ziyarci Cocin Joseph Chatholoc Da Ke Samarun Zariya

Daga Yusuf Kabir kabiruyusuf533@gmail.com Da safiyar  ranar Litinin 25/12/2023 ne wakilan 'yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zak...

Daga Yusuf Kabir kabiruyusuf533@gmail.com

Da safiyar  ranar Litinin 25/12/2023 ne wakilan 'yan uwa Musulmi Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky na garin Samarun Zariya suka ziyarci Cocin TJ.JOSEPH  CHATHOLIC da ke Samarun domin taya Kiristoci murnar bikin Kirsimeti na bana.

Wakilin Matattarar Labarai ya labarta mana cewa, a lokacin isar tawagar, ta samu gaharumar tarba daga masu kula da Cocin. 

Malam Jamilu Habibu Basawa ne ya yi bayanin dalilin ziyarar cikin harshen Turanci, Sannan ya miĈ™a abin magana ga Husaini Imam Mansu, wanda shi kuma ya gabatar da tawagar da suka kai ziyarar.

Bayan haka, sai aka miĈ™a abin magana ga Farfesa Isah Hasan Mshelgaru na Ahmadu Bello ta Zariya domin yin bayanin hadafin ziyarar.

Shehin Malamin Jami'ar ya bayyana dalilin ziyarar cikin harshen Turanci, inda ya bayyana cewa, ''Mun zo ne domin taya ku murnar haihuwar wannan bawa na Allah, wanda shi da Mahaifiyarsa sun kasance ayoyi na Allah a cikin halittarsa.

''HaĈ™iĈ™a addinin Musulunci da addinin Kiristanci dukkaninsu suna da alaĈ™a da juna, kuma mabiyansu su ne galiban mutanen da ke rayuwa a Nijeriya.

"Mu Almajiran Shaikh Ibraheem Ya'qoub Zakzaky (h) ne. A wajen mu dukkanin mutane abin girmamawa ne, domin ko dai 'yan uwan mu a addini ne, ko kuma 'yan uwan mu a halitta."

Farfesan ya ce, sun shekara 25 su na kai irin wannan ziyarar ga Cocina mabambanta a duk sassan Ĉ™asar nan, musamman a jihohi Arewa,  kuma hakan yana da matuĈ™ar amfani. Bugu da Ĉ™ari, hanya ce ta kusantar ma'abuta addinan biyu don samar da zaman lafiya da juna.''

Bayan kammala jawabin Farfesa Isah, sai aka gabatar da Fitaccen mawakin Harkar Musulunci Malam Ammar ĈŠantinka Zariya, inda ya rero daɗaɗan baituka ga Annabi Isah Almasihu (as), a yayin da makaɗan Cocin suka kiɗa gangunan su domin Ĉ™ara wa waĈ™ar armashi.

Bayan kammala waĈ™en, an gabatar da Dr. Salisu Ahmad, Malami a Jami'ar Umaru Musa 'Yar Aduwa domin ya Ĉ™addamar da kyautukan da maziyartan suka kai wa masu hidimar bikin. A yayin da Faston Cocin da ɗansa suka karɓa cikin farin ciki da annashuwa.

Daga nan ne kuma sai aka miĈ™a abin magana ga  Malam Jamilu Habibu Basawa, a yayin da ya gayyato Faston Cocin haɗe da Farfesa Isah Hasan Mshelgaru, Dr. Salisu Ahmad, Alhaji Mansur Ali, Ammar ĈŠantinka suka yanka Alkaki cikin farin ciki.

Bayan kammala hakan, ɗaya daga cikin Shugabannin Cocin ya yi bayanin godiya, inda ya miĈ™a abin magana ga Fasto ya yi bayani mai ratsa jiki da nuna jin daɗi ga ziyarar da 'yan uwa Musulmi suka gabatar, inda ya bayyana jin daɗin karramawar da aka yi musu, ciki kuwa har da yanka Alkaki.

Wani abin da wakilinmu ya lura da shi da  ya Ĉ™ara wa ziyarar armashi, shi ne gayyatar wakilan kafafen yaɗa labarai daban daban-daban da aka yi domin su ɗauki rahotannin ziyarar, tare da watsawa cikin al'umma.

Malam Bello Hamza Editan Jaridar Leadership Hausa, Mustapha Yawuri daga kafar NAN (tare da tawagarsa), Sagir Hunkuyi daga NTA, Yusuf Kabir daga Jaridar Almizan na cikin 'yan Jaridar da suka rufa wa tawagar baya.

Waɗanda aka kai wa ziyarar sun nuna matuĈ™ar farin cikin su.

 

No comments