Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Samar Da Tsaro: Gwamnatin Zamfara Na Bakin Ƙoƙarin Ta -Bashir Nafaru

Daga Imrana Abdullahi  Wani jagoran al'umma a Jihar Zamfara, kuma fitaccen ɗan siyasa daga Ƙaramar Hukumar Talatar Mafara, Alhaji Bashir...

Daga Imrana Abdullahi 

Wani jagoran al'umma a Jihar Zamfara, kuma fitaccen ɗan siyasa daga Ƙaramar Hukumar Talatar Mafara, Alhaji Bashir Nafaru ya bayyana cewa gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagorancin Dauda Lawal ta na iyaka ƙoƙarin ta wajen samar wa da al'umma tsaro a duk faɗin jihar.

Alhaji Bashir ya bayyana haka ne a zantawar sa da wakilin mu, inda ya ce, suna godiya ga Allah maɗaukakin Sarki, ganin cewa duk da matsalar tsaron da ake fama da ita a jihar, amma gwamnatin na yin iyakar bakin ƙoƙarinta.

Amma sai dai duk da wannan ƙoƙari na gwamnatin, Alhaji Bashir ya nemi da ta ƙara himma, "Don haka muke roƙon gwamnati domin Allah a taimaka wa talakawan da suke cikin daji 'yan uwan mu, domin babu abin da ake buƙata sai a samu ingantaccen tsaro, saboda rayuwar Talakawa na cikin wani hali na rashin tabbas.  Yanzu za a gaisa da mutum, ɗan anjima sai ka ji na ce an kashe shi kawai."

Game da ayyukan raya ƙasa kuwa, Alhaji Bashir Nafaru kira ya yi ga Gwamna Lawal da ya watsa ayyukan sa zuwa dukkan Ƙananan Hukumomin jihar 14, "Domin muna ganin kamar a Ƙaramar  Hukumar Gusau ce kawai ake aiwatar da ayyukan raya ƙasa. 

"Saboda haka ne muke ƙara yin kira ga gwamnati da ta duba matsalolin sauran Ƙananan Hukumomi Goma sha uku a san abin da za a yi masu."

No comments