Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Zamfara Ya Amince Da Biyan Ma'aikata Ƙarin Albashin Wata Ɗaya

Daga Musa Muhammad  Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya amince da biyan ma'aikatan jihar ƙarin albashi na wata ɗaya, wanda a Turanci ...

Daga Musa Muhammad 

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya amince da biyan ma'aikatan jihar ƙarin albashi na wata ɗaya, wanda a Turanci ake kira da '13th month salaries.' Wannan yana nuni ke nan da cewa ma'aikatan jihar za su sake samun wani ƙarin kashi 30 ciki 100 na albashin su a wannan wata na Disamba. 

A ranar Alhamis ɗin nan ne gwamnatin jihar ta sanar da yanke shawarar biyan wannan albashi na '13th Month Salary' cikin wata takarda mai ɗauke da sa hannun Shugaban Ma'aikatan jihar, Ahmed Aliyu Liman, wacce kuma aka rarraba ga ma'aikatun jihar da manema labarai.

Da ya ke ƙarin haske kan wannan ci gaba da ma'aikatan jihar suka samu, mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya bayyana cewa ba a taɓa samun irin wannan tagomashi ba, tun da aka kafa jihar Zamfara. 

Idris ya ce, yanke wannan shawarar ta zo daidai ne da aniyar gwamnatin na kyautata wa jin daɗin ma'aikatan jihar don inganta ayyukan su na samun sakamako mai kyau. 

Sanarwar ta Kakakin Gwamnan ta ci gaba da bayyana cewa, “A yau Gwamna Lawal ya imince da biyan garaɓasar ƙarshen shekara ga ma'aikatan gwamnatin jihar Zamfara. 

“Manufar wannan tagomashi, shi ne do ƙara inganta rayuwar ma'aikatan, sannan a samar masu da 'yan kuɗaɗen da za su yi hutu cikin sukuni. 

“Ba wani abu ba ne wannan, kasancewar shi ne karo na farko da aka taɓa biyan ma'aikatan jihar Zamfara ƙarin albashin wata ɗaya a tarihin jihar. 

“Wannan alama ce da ke nuna aniyar Gwamna Dauda Lawal ta inganta yanayin aikin jihar, ƙarin albashi da samar da yanayi mai kyau ga ma'aikatan gwamnatin.  

“Biyan wannan ƙarin albashi na '13th-month salary' ɗaya ne daga dubban tsare-tsaren da ake da su da nufin tallafa wa ma'aikatan da inganta tattalin arzikin jihar Zamfara."

 

 

No comments