Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya tsige Shugaban Hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta jihar, Dakta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu, inda k...
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya tsige Shugaban Hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta jihar, Dakta Yusuf Yakubu Arrigasiyyu, inda kuma nan take ya naɗa Malam Salihu S. Abubakar a matsayin sabon shugaban Hukumar mai cikakken iko.
Wannan yana ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren yaɗa labaran Gwamnan, Muhammad Lawal Shehu ya sanya wa hannu yau Lahadin nan.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa wanda ya zama matsayin Sakatare a kwamitin nan na musamman kan aikin hajjin 2024, shi ne zai zama Sakataren Hukumar, sannan sauran mambobin Kwamitin za su kasance mambobin hukumar gudanarwar Hukumar Alhazan.
Muhammad Lawal ya ci gaba da bayyana cewa, shi kuma Dakta Arrigasiyyu an mayar da shi Shugaban Hukumar kare muhalli ta jihar, (KEPA).
No comments