A wani abu da ya faranta wa Palaɗinawa rai, Yarima Mohammed Bin Salman na Saudi Arebiya da Shugaban Turkiyya, Raceb Tayyib Erdogan sun yi ...
A wani abu da ya faranta wa Palaɗinawa rai, Yarima Mohammed Bin Salman na Saudi Arebiya da Shugaban Turkiyya, Raceb Tayyib Erdogan sun yi kakkausar suka kan Isra'ila bisa kisan ta'addancin da suke yi wa Palaɗinawa.
Yarima Muhammad ya kuma ɗora ta Isra'ilar alhakin abin da ya kira "laifukan da ake tafkawa a kan Falasɗinawa."
Daga nan sai Yariman ya yi kira da a kawo ƙarshen mamayar da aka yi wa Zirin Gaza, tare da samar da ƙasar Falasɗinawa bisa yarjejeniyar 1967.
Shi ma Erdogan na Turkiyya bayyana Ira'ila a matsayin sangartacciyar ƙasa.
Sakamakon wannan ci gaba, Sarki Abdallah II na Jordan da kuma shugaban Falasɗinawa duk sun amince da batun na yariman na Saudiyya da Turkiyya.
Ya yi kira ga ƙasashe da su fito fili su yi magana kan rashin abin da ke faruwa a Gaza, da kuma buƙatar Isra'ila ta biya diyya ga Falasɗinawa.
Haka nan ya buƙaci a hukunta Isra'ila kan laifukan da ta aikata kan Falasɗinawa.
.jpg)
No comments