Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Amarya Ta Yi Wa Angon Ta Yankan Rago A Kano

Ana zargin wata sabuwar amarya da yanke maƙogwaron angonta har lahira, ƙasa da wata biyu da aurensu a Jihar Kano. Shaidu sun bayyana cewa am...




Ana zargin wata sabuwar amarya da yanke maƙogwaron angonta har lahira, ƙasa da wata biyu da aurensu a Jihar Kano.

Shaidu sun bayyana cewa amaryar ta aikata wannan aika-aika ne a unguwar Rimin Kebe, inda ake zargin ta daɓa wa angonta, Auwalu, wuƙa har ya ce ga garinku nan.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi bayan wata gardama da ta taso tsakanin sabbin ma’auratan, waɗanda majiyoyi suka ce ba auren soyayya suka yi ba.

Wani mazaunin unguwar, wanda ya nemi a ɓoye sunansa, ya shaida wa manema labarai cewa tun da farko mamacin ya yi ihu yana neman agaji bayan da aka kai masa hari.

Majiyar ta ce matar ta daɓa wa mijin wuƙa ne saboda abin da ta kira auren dole, tana mai cewa ba ta taɓa ƙaunar sa ba.

“Fatima ta daɓa masa wuƙa a wuya. Ya fito yana ihu cewa matarsa ce ta daɓa masa. Aka garzaya da shi ofishin ’yan sanda sannan daga bisani aka wuce da shi asibiti, amma ya rasu kafin a isa asibitin,” in ji majiyar.

Nan take jami’an ofishin ’yan sanda na Zango a Ɗantamashe suka kama wadda ake zargi.

Majiyarmu ta ƙara da cewa, “Auren nasu bai kai wata biyu ba. Yanzu matar tana tsare a hannun ’yan sanda.”

No comments