Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

’Yan Sanda Sun Kama Matashi Ɗauke Da Hannun Mutum Da Bindigogi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta kama wani matashi mai shekara 21, Samson Onilewaji bisa zargin fashi da makami, bayan an gano wani hannu...




Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta kama wani matashi mai shekara 21, Samson Onilewaji bisa zargin fashi da makami, bayan an gano wani hannun mutum, bindigogi da wasu kayayyakin da ake zargin na sata ne a hannunsa.

Kakakin rundunar, SP Abimbola Adebisi ta ce an kama wanda ake zargin ne yayin wani binciken abubuwan hawa da jami’an ’yan sanda suka gudanar a kan titin Lekki zuwa Epe.

Ta ce, binciken ya kai ga gano wani hannun dama na mutum da ake zargi, bindigogi biyu ƙirar gida da harsashi da gatari biyu da na’urar POS da katunan ATM guda biyar a hannunsa.

A cewarta, binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin ya amsa laifin hannu a wasu hare-haren fashi, inda aka ƙwato na’urar POS da katunan ATM da ake zargin ya ƙwace daga wasu mutane.

Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike domin gano mamallakin hannun mutumin da aka samu, da yadda ya shiga hannun wanda ake zargin tare da zaƙulo sauran waɗanda ake zargin suna da hannu a lamarin.

Ta ƙara da cewa, za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.

No comments