Ministan Harkokin Cikin Gida na Nijeriya, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kama wasu mutane bakwai da ake zargin ...
Ministan Harkokin Cikin Gida na Nijeriya, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun kama wasu mutane bakwai da ake zargin manyan kwamandojin Ęungiyoyin Boko Haram da ISWAP ne yayin da suke dawowa daga aikin Hajji.
A cewarsa, an cafke waÉanda ake zargin ne a filin jirgin saman Katsina a ranar Alhamis bayan sun iso daga Makka, kafin daga bisani a miĘa su ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) domin ci gaba da bincike. Ya ce nasarar wannan aiki ta samu ne sakamakon inganta tsarin tantance bayanan jama'a da kuma haÉa bayanan hukumomin gwamnati wuri guda.
Tunji-Ojo ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a Fadar Shugaban Ęasa da ke Abuja bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan sabuwar Dokar Hukumar Kula da Shaidar Ęan Ęasa ta Ęasa (NIMC) ta shekarar 2026.
A wajen taron sanya hannu kan dokar akwai Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio; Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu; Jagoran Majalisar Wakilai, Julius Ihonvbere; Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Yarima Lateef Fagbemi; wakilin Bankin Duniya, Taimur Samad; da Darakta Janar ta Hukumar NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai Wa Shugaban Ęasa Shawara kan YaÉa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, gwamnatin tarayya ta bayyana sabuwar dokar a matsayin wani muhimmin mataki na zamanantar da tsarin tantance bayanan jama’a, Ęarfafa tsaro, inganta samar da ayyukan gwamnati da kuma bunĘasa tattalin arzikin dijital na Ęasa.
Da yake jawabi bayan rattaba hannu kan dokar, Ministan Harkokin Cikin Gida ya ce wannan doka za ta taimaka matuĘa wajen Ęarfafa tsaron cikin gida da kuma sauĘaĘa wa ‘yan Ęasa samun ayyukan gwamnati.
Ya bayyana cewa gwamnatin Shugaba Tinubu ta gaji wani tsarin bayanan jama’a da ya rarrabu, inda mahimman bayanai ke aiki ba tare da alaĘa da juna ba. Sai dai ya ce yanzu an samu haÉin kai tsakanin manyan cibiyoyin bayanan gwamnati.
“Lokacin da wannan gwamnati ta hau mulki, tsarin bayananmu ya kasance a rarrabe. Samun fasfo da lasisin tuĘi ba su da alaĘa da bayanan NIMC. Amma yanzu ba za ka iya samun fasfon Nijeriya ba sai an tantance bayananka daga NIMC,” in ji shi.
Tunji-Ojo ya Ęara da cewa haÉa bayanan hukumomi ya taimaka wajen Ęarfafa kula da iyakokin Ęasa da kuma tattara bayanan sirri na tsaro.
Ya tuna cewa a baya wasu manyan jami’ai sun nuna damuwa kan yadda wasu ‘yan ta’adda suka samu damar zuwa aikin Hajji. Sai dai ya ce sabon tsarin da aka kafa ya taimaka wajen gano waÉanda ake nema.
“Makon da ya gabata ne aka kama wasu mutum bakwai da ake da bayanan cewa kwamandojin Boko Haram da ISWAP ne yayin da suke dawowa daga Makka ta filin jirgin saman Katsina. Daga nan aka miĘa su ga DSS,” in ji ministan.
Ya bayyana cewa wannan nasara ta samu ne saboda haÉa bayanan NIMC da na Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, tare da tsarin sadarwa kai tsaye da Hukumar ‘Yan Sandan Duniya (Interpol) ke yi da hukumomin Nijeriya.
Ministan ya ce sabuwar dokar za ta taimaka wajen Ęara ingancin lambar shaidar Éan Ęasa ta NIN, Ęarfafa haÉin gwiwar hukumomi, da kuma yaĘi da satar bayanan jama’a, ta’addanci, laifukan kuÉi da sauran barazanar tsaro.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya yaba da amincewar Shugaban Ęasa da dokar, yana mai cewa hakan ya nuna aniyar Majalisar Tarayya wajen samar da dokokin da suka dace da Ęalubalen tsaro da ci gaban Ęasa.
Shi ma Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, ya bayyana dokar a matsayin wani babban sauyi da zai inganta shugabanci, gaskiya da riĘon amana tare da taimakawa ci gaban Ęasa ta hanyar ingantaccen tsarin tantance bayanan jama’a.
A nata Éangaren, Darakta Janar ta NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote, ta tabbatar da cewa hukumar za ta yi aiki tare da sauran hukumomi, abokan hulÉar ci gaba da kamfanoni masu zaman kansu domin tabbatar da aiwatar da dokar yadda ya kamata.
Ta ce dokar ta samar da sabon tsarin doka na zamani ga tsarin bayanan dijital na Nijeriya, tare da Ęarfafa matsayin lambar NIN a matsayin babbar hanyar tantance shaidar Éan Ęasa da samun ayyukan gwamnati da na masu zaman kansu.

No comments