Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Obi Da Kwankwaso Sun Shiga Ruɗani Bayan Kotu Ta Soke Rajistar Jam'iyyar NDC

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Lokoja ta soke hukuncin da ta yanke a baya wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ...




Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Lokoja ta soke hukuncin da ta yanke a baya wanda ya umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta yi wa jam’iyyar NDC rajista a matsayin jam’iyyar siyasa, lamarin da ya buɗe ƙofar sake sauraron shari’ar daga tushe.

Rahotanni sun nuna cewa tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC.

A hukuncin da Mai Shari’a Isah Dashen ya yanke a ranar Juma’a, ya bayyana cewa hukuncin da kotun ta bayar a ranar 10 ga Disamban 2025 ya shafi haƙƙin jam’iyyar Peace Movement Party (PMP), wadda ba a shigar da ita cikin shari’ar ba duk da cewa tana ikirarin mallakar tambarin da NDC ta yi amfani da shi wajen neman rajista.

Saboda haka, kotun ta umarci dukkan ɓangarorin da abin ya shafa su koma matsayin da suke kafin yanke hukuncin farko, tare da umartar masu shigar da ƙara su haɗa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa domin a yi cikakken nazari da yanke hukunci cikin adalci.

Lauyan jam’iyyar PMP, C.S. Ekeocha, ya bayyana cewa jam’iyyarsa ta nemi shiga shari’ar ne bayan gano cewa NDC ta yi amfani da tambarin da PMP ta gabatar wa INEC tun kafin fara shari’ar.

A cewarsa, rashin shigar da PMP cikin karar da aka yi tun farko ya hana jam’iyyar damar kare kanta, duk da cewa hukuncin ya shafi muradunta kai tsaye.

Ya ce kotun ta umarci a dawo da komai yadda yake kafin hukuncin Disamban 2025, tare da ba da umarnin a haɗa PMP da sauran masu ruwa da tsaki domin a saurari kowa kafin a sake yanke hukunci.

Lauyan ya ƙara da cewa duk matakan da INEC ta ɗauka bisa tsohon hukuncin kotun yanzu sun tsaya cik har sai an kammala sauraron sabon shari’ar.

Hakan ya haɗa da amincewa da NDC a matsayin jam’iyyar siyasa, bayar da takardar rajista, sanya sunanta cikin kundin jam’iyyun siyasa na INEC da kuma duk wani mataki da ya samo asali daga hukuncin farko.

A cewarsa, waɗannan matakai za su ci gaba da kasancewa a dakace har sai kotu ta yanke hukunci na ƙarshe bayan sauraron dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.

No comments