Hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC Ta bayyana cewa an jawo hankalin ta game da wasu takardun sakamakon zaɓe waɗanda aka riga aka cika tun kafin a ...
Hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC Ta bayyana cewa an jawo hankalin ta game da wasu takardun sakamakon zaɓe waɗanda aka riga aka cika tun kafin a jefa ƙuri'a a wasu runfunan zaɓe a jihar Kogi.
Hukumar ta yi wannan nun nei a kafar yaɗa labarin ta ta tweeter, inda ta ce "Hukumar mu na ɗaukar wannan lamari da muhimmanci, kuma ba za mu yi wasa da shi ba."
Ta ce, ta tura da manyan jami'anta zuwa jihar Kogin don binciko sahihancin labarin, za kuma ta sanar da matakin ɗauka.

No comments