Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya tabbatar wa masu sha'awar zuba jari a ƙasar nan daga Saudiyya da cewa su hanzarta yin haka, domin ...
Shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu ya tabbatar wa masu sha'awar zuba jari a ƙasar nan daga Saudiyya da cewa su hanzarta yin haka, domin akwai aminci da yanayi mai kyau a ƙasar.
Mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ne ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, inda ya ce Tinubu ya bayar da wannan tabbacin ne a Riyadh ta Saudi Arebiya wajen wani taron tattalin arziki da aka gudanar cikin makon nan.
Ngalale ya ce, Shugaba Tinubu ya ƙara jaddada wa duniya cewa Nijeriya a shirye ta ke wajen tarbar duk wani mai sha'awar zuba jari, kuma akwai samun riba gwaggwaɓa.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya nemi haɗa hannu da ƙasar ta Saudi Arebiya wajen maganin ta'addanci, musamman Boko Haram, ISWAP da 'yan ta'adda masu tsattsauran ra'ayin addini da suka addabi yankin Chadi.
Ya ce, Nijeriya da Saudi Arebiya sun jima suna amfanar juna ta hulɗar dangantaka a tsakaninsu su biyu da taron sauran ƙasashe.
"Ina ƙara tabbatar wa da duk wani Basa'udiyye da ke da sha'awar zuba a Nijeriya kan ya hanzarta yin haka, domin akwai yanayi mai kyau a ƙasar, musamman irin tsare-tsaren da gwamnati ta yi, sannan za a sami sakamako mai kyau.
Daga nan ya gode wa ƙasar ta Saudiyya bisa irin taimakon jin ƙan da ta ke bayarwa a fannoni daban-daban a ƙasar, ta hannun cibiyar nan ta bayar da agaji ta " King Salman Humanitarian Aid and Relief Centre."

No comments