Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC), ta dakatar da zaɓe a wasu yankunan Jihar Kogi sakamakon yadda aka tafka kura-kurai a zaɓ...
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC), ta dakatar da zaɓe a wasu yankunan Jihar Kogi sakamakon yadda aka tafka kura-kurai a zaɓen, musamman lamarin da ya faru na cike takardar sakamakon zaɓe kafin fara kaɗa ƙuri’a.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ƙananan hukumomin Adavi, Ajaokuta, Ogori/Magongo, Okehi da Okene. Lamarin da ya fi ƙamari ya faru ne a yankin Ogori/Magongo, wanda ya shafi yankuna tara daga cikin 10 da aka yi rajistar zaɓe.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da Mohammed Haruna, Kwamishinan Kasa kuma Shugaban Watsa Labarai da Ilimantar da Masu Zaɓe ya fitar a Asabar, 11 ga Nuwamba, 2023
Sanarwar ta ce, "wannan sam ba za a yarda da shi ba. Duk wani sakamakon da bai fito daga tsarin hukumar ba a rumfunan zabe, ba za a amince da shi ba."
"Hukumar ta ƙuduri aniyar ladabtar da masu munanan halaye. Sakamakon haka, a halin yanzu an dakatar da zaben a Unguwa Tara da ke laramar hukumar Ogori/Magongo (Eni, Okibo, Okesi, Ileteju, Aiyeromi, Ugugu, Obinoyin, Obatgben da Oturu). Ana ci gaba da gudanar da bincike sosai kan abubuwan da suka faru a sauran kananan hukumomin, kuma za a sanar da sakamakon da aka samu ciki har da hanyar da za a bi nan da sa’o’i 24 masu zuwa", inji sanarwar.
"A halin yanzu, yayin da tsarin ke cigaba, muna bin sawu na tantance ma'aikata da kayan aiki don tabbatar da wadanda ke da hannu wajen lalata tsarin. Muna da bayanan duk jami'an da aka tura a matakai daban-daban a matsayin masu kulawa, masu sa ido, ma'aikatan fasaha ko jami'an rumbun zabe da duk kayan zabe da aka ba su. Za a yi amfani da duk bayanan da suka dace a inda ya cancanta."
Hukumar ta tabbatar wa masu kada kuri’a a jihar Kogi cewa an kare kuri’unsu, kuma za a mutunta buƙatunsu.
No comments